Amurka ta sanar da ba da tallafin dala miliyan 203 don ƙarin taimakon jinƙai ga Sudan

Amurka ta sanar da ba da tallafin dala miliyan 203 don ƙarin taimakon jinƙai ga Sudan

Jakadiyar Amurka a MDD Linda Thomas-Greenfield ta ce al'ummar Sudan na fuskantar matsalar jinƙai mafi muni a duniya.
“Yara sun yi rauni sosai kuma ba su da kuzarin yin kuka saboda tsananin yunwa," in ji  Linda Thomas-Greenfield / Hoto: Getty Images

Amurka ta sanar da ba da tallafin sama da dala miliyan 200 a matsayin ƙarin tallafin jinƙai ga fararen hula a Sudan da kuma wadanda suka yi gudun hijira zuwa ƙasashe maƙwabta.

Taimakon ya hada da sama da dala miliyan 178 daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka da kuma kusan dala miliyan 25 ta hannun Hukumar Raya Ƙasashe ta Amurka (USAID).

“Mutanen Sudan na fuskantar matsalar jinƙai mafi muni a duniya. Ana buƙatar sa hannu da yawa don taimaka musu.

"Ina farin cikin sanar da cewa Amurka na bayar da ƙarin dala miliyan 203 a matsayin taimakon jinƙai, domin tallafa wa mutanen Sudan da Chadi da Masar da Sudan ta Kudu da wannan mummunan rikici ya shafa,” kamar yadda jakadiyar Amurka a MDD Linda Thomas-Greenfield ta shaida wa manema labarai.

"Muna fatan wannan sabon zagaye na taimakon ya zama kira ga wasu su yi koyi."

Yayin da take bayyana cewa har yanzu mashigar kan iyakar Eritrea a rufe take, daya daga cikin muhimman abubuwan da suka shafi agajin jinƙai, ta ce: "Wannan cikas ba abu ne da ba za a amince da shi ba."

Jakadiyar ta ce ƙarin dalar Amurka miliyan 203 din za ta hada da kayan abinci da samar da matsuguni da makarantu da ayyukan kiwon lafiya, da kuma tallafin kudi ga 'yan gudun hijirar don taimakawa wajen biyan kudin haya.

Kudaden kuma za su taimaka wa kasashe maƙwabta da aka lissafa a sama, inda sama da 'yan gudun hijirar Sudan miliyan biyu suka tsere can, in ji ta.

Tawagar Amurka a MDD ta ce Thomas-Greenfield ta yi wa jami'an diflomasiyyar MDD bayani kan matsalar yunwa a Sudan, inda mutum miliyan 25 ke fuskantar matsalar ƙarancin abinci, yayin da mutum 755,000 ke fuskantar yunwa a cikin watanni masu zuwa, a cewar wani rahoto na baya-bayan nan da hukumar sa ido kan barazanar yunwa ta MDD ta fitar.

Ƙwararru kan kare hakkin ɗan'adam da ke aiki da MDD sun ce bangarorin biyu da ke faɗa da juna a Sudan sun yi amfani da abinci da yunwa a matsayin makaman yaƙi.

Thomas-Greenfield ta tuna ziyarar da ta kai wani asibiti a Chadi da kungiyar agaji ta Doctors Without Borders ke gudanarwa, inda ta ce: “Yara sun yi rauni sosai kuma ba su da kuzarin yin kuka saboda tsananin yunwa.”

TRT Afrika da abokan hulda