Amurka ta ɗaure ɗan gidan tsohon shugaban Guinea-Bissau kan miyagun ƙwayoyi

Amurka ta ɗaure ɗan gidan tsohon shugaban Guinea-Bissau kan miyagun ƙwayoyi

Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta ce Malam Bacai Sanha mai shekara 52 ya amsa laifukan da ake zarginsa da su.
Guinea-Bissau na da tarihin juyin mulki. / Hoto: Reuters

Amurka ta yanke wa tsohon ɗan gidan shugaban Guinea-Bissau hukuncin zaman gidan yari na sama da shekara shida a gidan yari bayan samunsa da laifin safarar miyagun ƙwayoyi.

Ma’aikatar Shari’ar Amurka ce ta tabbatar da hakan a ranar Talata inda ta ce Malam Bacai Sanha, mai shekara 52, ya yi niyyar amfani da kuɗin ƙwayoyin domin ɗaukar nauyin juyin mulki a ƙasar da ke yammacin Afirka.

Idan Mista Macai ya yi hakan zai samu damar ɗarewa kujerar shugaban ƙasa a Guinea-Bissau, in ji sanarwar da Babban Lauyan Gwamnati na Gundumar Texas ta Amurka ya fitar.

“Malam Bacai Sanha ba kowane irin mai safarar ƙwayoyi ba ne,” in ji Douglas Williams, wanda jami’i ne na musamman da ke kula da ofishin FBI na Houston.

“Ɗa ne ga tsohon shugaban Guinea-Bissau kuma yana safarar ƙwayoyi ne saboda wani dalili – domin taimaka wa juyin mulki.”

Sanha ya kasance jagora kuma mai shirya makircin safarar heroin kuma yana da hannu wajen shigo da ƙwayoyi daga Turai zuwa Amurka, a cewar sanarwar.

An kama shi ne tare da wani abokin burminsa bayan ya isa birnin Dar es Salaam na kasar Tanzaniya a watan Yulin 2022. An mika su Amurka jim kadan bayan haka.

AFP