Tun daga ranar 15 ga watan Afrilu, Babban Hafsan Soji kuma shugaban kasa Abdel Fattah al Burhan ya fara yaki da tsohon mataimakinsa Kwamandan dakarun Rapid Support Forces (RSF) Mohamed Hamdan Daglo. / Hoto: AP      

Duka bangarori biyu da ke yaki da juna a Sudan sun aikata laifukan yaki tun farkon soma yakin a watan Afrilun, in ji Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Amnesty International.

Kungiyar ta bayyana haka ne a wani rahoto da ta fitar ranar Alhamis cewa laifukan da janar biyu da ke jagoranta yakin suka aikata sun hada da na cin zarafin kananan yara da kai wa fararen-hula hari.

"An aikata manyan laifukan yaki a Sudan yayin da yaki ya ci gaba da kassara kasar," in ji rahoton Amnesty International, wanda ya ci gaba da cewa "fararen-hula da dama ne yakin ya rutsa da su da gangan da kuma bisa kuskure daga bangarorin biyu da ke yaki da juna".

Ya ce hare-haren da bangarorin suke kai wa juna suna rutsawa da mata da kuma yara a wurare masu cunkoso, inda ake amfani da abubuwan fashewa da ke shafar wuri mai fadi.

A bayanan da Amnesty International ta tattara, mutanen da suka tsira sun ce dakarun RSF ko kungiyoyi masu dauke da makamai da ke goya musu baya ne ke kai musu hari.

A rahotonta, Amnesty ta ce ta gana da fiye da mutum 180 a gabashin Chadi, inda 'yan gudun hijira da suka tsere daga Darfur suke samun mafaka.

Amnesty ta ce tana zargin sojoji da dakarun RSF, wadanda duka suka ce "suna mutunta dokokin kasa da kasa kuma kowannensu ya zargi dayan bangaren da take doka".

'Tashin hankali da ba ya misaltuwa'

Tun daga ranar 15 ga watan Afrilu, Babban Hafsan Soji Abdel Fattah al Burhan ya fara yaki da tsohon mataimakinsa Kwamandan dakarun Rapid Support Forces (RSF) Mohamed Hamdan Daglo.

"Fararen-hula a gaba dayan Sudan suna shiga mawuyacin halin da ba ya misaltuwa a kowace rana yayin da dakarun Rapid Support Forces (RSF) da Sojojin Sudan suke ci gaba da kokarin karbe iko da wurare," in ji Sakatariya Janar ta Amnesty International Agnes Callamard.

"Dole ne RSF da Sojojin Sudan da kungiyoyin da ke mara musu baya su kawo karshen kai wa fararen-hula hari kuma su ba su tabbacin samar musu da hanyar da za su iya fita," in ji ta.

Burhan ya hau mulki ne tare da Dagalo a matsayin mataimakinsa a juyin mulkin watan Oktoban 2022 wanda ya kawo cikas ga gwamnatin rikon kwarya da aka shirya za ta mika mulki ga farar-hula, bayan sojoji sun hambarar da gwamnatin Shugaba Omar al Bashir a watan Afrilun 2019 bayan wata zanga-zanga da aka yi.

Amma daga bisani mutanen biyu sun samu sabani.

Yakın – wanda aka fi yi a birnin Khartoum da Darfur wanda ke yammacin kasar – ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 4,000, kamar yadda wata kungiya mai zaman kanta mai suna ACLED ta bayyana.

Kazalika yakin ya raba mutum fiye da miliyan 3.3 da muhallinsu, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

AFP