Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya (NEMA) ta bayyana cewa kawo yanzu ambaliyar ruwa ta shafi mutum 227,494 a jihohi 27 a faɗin ƙasar.
A ƙiyasin da ta yi game da asarar da ambaliyar ruwan ta haifar, NEMA ta ce gidaje 32,837 da kadada 16,488 na gonaki da amfanin gona ne iftila'in ruwan ya lalata, a cewar wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X ranar Alhamis.
NEMA ta yi gargaɗi ga mazauna yankunan da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a jihohin 27 da su soma ƙaura zuwa wasu wurare masu tsaro, kamar yadda mai magana da yawun Hukumar Mr. Manzo Ezekiel ya bayyana a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja.
"NEMA ta soma gudanar da aikin tantance yawan ɓarnar da ambaliyar ruwa ta yi tare da tura kayan agaji don tallafa wa al'umomin da iftila'in ya shafa," in ji shi.
Shugabar Hukumar, Zubaida Umar, ta jaddada buƙatar ɗaukar matakan gaggawa ga al’umomin yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa, tana mai ba da shawara da su koma wurare masu tudu yayin da ake cikin damina.
Kazalika shugabar ta yi kira kan a ƙara wayar da kawunan jama’a kan matakan da suka kamata su bi wajen kwashe shara don hana aukuwar ambaliyar ruwa a nan gaba.
"Hukumar ta jaddada muhimmancin wayar da kan jama'a game da hanyoyin sarrafa shara don hana ambaliyar ruwa tare da ba da shawara ga al'ummomin da ke cikin haɗarin fuskantar iftila'in da su koma wurare masu tudu da ba su da barazanar fuskantar ambaliyar," in ji sanarwar.
NEMA ta kuma buƙaci masu ruwa da tsaki, musamman hukumomin bayar da agajin gaggawa a matakin jihohi (SEMA) da shugabannin al'umomi, da su kasance cikin shiri a ko da yaushe don samar da tsare-tsare da shirin ko-ta-kwana kan ambaliya yayin da ake samun ƙaruwar iftila'in a wasu sassan Nijeriya.