Ambaliyar ruwa da ta auku sakamakon sauyin yanayi ta shafi sama da mutum 700,000 a ƙasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka a wannan shekarar kawo wannan lokaci, a cewar Ofishin Bayar da Jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya (OCHA) a ranar Talata.
Ambaliyar ruwa ta rusa ko kuma lalata gidaje sama da 60,000, inda ta tilasta wa mutane fiye da 54,000 ciki har da mata da yara barin muhallansu, in ji OCHA a wata sanarwa da ta fitar.
Kazalika ambaliyar ruwan ta rusa makarantu da asibitoci, lamarin da ya shafi samar da ilimi da kiwon lafiya.
Sanarwar ta ce mutum 72 ne aka bayar da rahoton mutuwarsu sakamakon nutsewa a ruwa sannan kusan mutum 700 sun jikkata.
Ƙasashen da ambaliyar ruwan ta shafa sun haɗa da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, Chadi, Ivory Coast, Jamhuriyar Dimokuraɗiyya Kongo, Laberiya, Nijar, Nijeriya, Mali da Togo.
Chadi ce ƙasar da ambaliyar ruwan ta fi yi wa illa, inda ta shafi sama da mutum 245,000 cikin makonni kaɗan.
“A duk shekara, muna yin gargaɗi game da illolin sauyin yanayi da kuma tasirinsu kan rayuwar jama'a -- gidajensu, harkokin noma, yadda za su tura yaransu makaranta da samun kiwon lafiya,” in ji Charles Bernimolin, babban jami'in ONCHA a Yammaci da Tsakiyar Afirka.
Ya ƙara da cewa, “Ya kamata a ɗauki matakai masu maa'ana domin tabbatar da ganin al'ummomi sun shirya wajen tunkarar wannan lamari ko kuma ma a yi rigakafin aukuwar bala'in".
Hukumomin da ke hasashen yanayi sun ce damunar 2024 za ta saukar da ruwan sama fiye da ƙima daga watan Yuni zuwa Satumba musamman a yankuna da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a ƙasashen yankin Sahel da na Yammacin Afirka.