Kwalekwale sun maye gurbin motocin da babura a kan hanyoyin sakamakon ambaliyar ruwa da tamamaye  Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar. / Hoto: AFP  

Manyan hanyoyin fita da shiga birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar mai kimanin mutum miliyan 1.5 sun kusan katsewa baƙi ɗaya, kana sama da mazauna birnin mutum 11,500 ne iftila'in ambaliyar ruwan sama ya shafa.

A watanni uku da suka wuce, ambaliyar ta yi sanadiyar mutuwar mutane 217 a faɗin ƙasar kana ta shafi sama da mutane 350,000, a cewar gwamnatin mulkin soji ta Nijar.

Da farko dai birnin Yamai ya tsira daga sauran yankunan kudu maso yammacin Nijar, amma a yanzu, kwale-kwale ne suka maye gurbin ƙanana da manyan motoci da babura wajen jigilar mutane da kayayyaki a kan hanyoyi.

Don samun damar isa zuwa ga sauran sassan ƙasar, ''dole sai mutum ya yi amfani da kwale-kwale tare da fatan samun abin hawa idan ya isa ɗaya bangaren,'' in ji Habibulaye Abdoulaye, wani mazaunin wata unguwa da ke kewaye da ruwa.

Yawancin kamfanonin sufuri a Yamai sun dakatar da zirga-zirga zuwa sauran sassan Nijar.

Yayin da yake kallon yadda ambaliyar ruwan ke gudu ta gefen birnin, wani direban mota Ali Adamou ya shaida wa kamfanin dillacin labarai Faransa AFP cewa ruwan ya tafi da motarsa tare da wasu guda hudu.

"Na kusan mutuwa a lokacin da wata ƙaramar motar bas ta nutse," in ji A damou

Gyara hanyoyi

Masu tuƙa ƙananan jiragen ruwa suna karɓar CFA 500 kan duk jigilar da suka yi sai kuma 'yan sanda da kwale-kwalen sojoji waɗanda suke taimakawa wajen jigilar mazauna da suka maƙale.

Daga gabashin babban birnin ƙasar, kamfanin gine-gine na ƙasar Faransa Sogea-Satom na ƙoƙarin sake buɗe hanyar ƙasa ta ɗaya, babbar hanyar da ta kai tsawon kilomita 1,500.

A gaɓar kogin Neja da ke birnin Yamai, masu aikin tono suna can suna aikin samar da hanyoyin wucewar ruwan, yayin da masu aikin sa kai da sojoji suke zagayawa don toshe wurare da ruwan ya yi wa illa da yashi.

A kwanakin baya ne aka sake buɗe hanya ɗaya tilo ta Tera da manyan motoci suke wucewa daga Yamai zuwa arewacin Burkina Faso.

"Hukumomin jihar suna yin dukkan mai yiwuwa don maido da zirga-zirgar ababen hawa," in ji Ministan Sufuri, Kanar Salissou Mahaman Salissou.

Hukumomin Nijar dai na fargabar tsawaita zirga-zirgar na iya haifar da ƙaranci man fetur.

AFP