Mamakon ruwan sama a Nijar ya yi ajalin mutane 339, tare da raba sama da miliyan 1.1 da matsugunansu tun daga watan Yuni zuwa yau, in ji kafar yada labarai ta kasar.
Ya zuwa 23 ga Satumba, ambaliyar ruwanta shafi sama da mutane miliyan 1.1, tare da yin ajalin mutane 339, inda wasu 383 kuma suka samu raunuka, in ji kamfanin dillancin labarai na kasar ANP a ranar Talata.
A watan da ya gabata ministan harkokin cikin gida ya bayyana cewa a kalla mutane 273 ne suk mutu sakamakon munanar yanayin da ya shafi mutane 700,000 a kasar ta yankin Sahel.
Ambaliyar ruwan ta shafi yankunan kasar da dama, ciki har da babban birnin Yamai inda mutane tara suka mutu.
Ambaliyar ta kuma janyo asarar kayayyaki, dabbobi da amfanin gona.
Ruwan sama ninkin yadda aka saba gani
Masallaci mai tarihi a kasar ta Musulmai da ke garin Zinder da aka gina a tsakiyar karni na 19 ya rushe.
Wasu yankunan kasar sun samu mamakon ruwan sama ninkin yadda aka saba gani a shekarun baya, kamar yadda hukumar kula da yanayi ta kasar ta bayyana.
Sakamakon matsalolin da makarantu suka samu da yadda ibtila'in ya tsugunar da iyalai, gwamnati ta dage lokacin koma wa makarantu har nan da karshen watn Oktoba.
A lokacin damina a Nijar da ke zuwa daga watan Janairu zuwa Satumba, ana yawan samun mamakon ruwan sama, inda mutane 195 suka mutu a 2022.
Tun tuni masana kimiyya suka yi gargadi kan sauyin yanayi da dattin hayakin fosil ke janyo wa, wanda hakan kuma ke sa a samu ambaliyar ruwa da ke yin tasiri marar kyau a yankunan duniya daban-daban.