NDLEA ta ce tana zargin tsohuwar sarauniyar ta kyau da tu'ammali da miyagun ƙwayoyi. / Hoto: NDLEA

Hukumar Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta bayyana cewa tana neman wata tsohuwar sarauniyar kyau ruwa a jallo.

Wadda ake zargin ita ce Sarauniyar Kyau ta Nijeriya ta Kungiyar Kasashen Rainon Ingila ta 2015/2016 kuma ita ce ta ƙirƙiro gidauniyar Queen Christmas Foundation.

Hukumar ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi inda ta ce tana zargin Ms. Aderinoye Queen Christmas wadda aka fi sani da Ms. Queen Oluwadamilola da tu’ammali da miyagun ƙwayoyi.

NDLEA ta ce tsohuwar sarauniyar ta kyau ta tsere daga gidanta da ke unguwar Lekki a birnin Legas a daidai lokacin da jami’an hukumar suka kai mata samame a ranar Laraba 24 ga watan Janairun 2024.

Hukumar ta ce jami’an nata sun kai samamen ne sakamakon sahihan bayanan sirri da suka samu kan cewa tana tu’ammali da miyagun ƙwayoyi.

NDLEA ta ce daga cikin abubuwan da aka gano a gidan Ms. Aderinoye sun haɗa da gram 606 na wani samfurin wiwi mai suna Canadian Loud, haka kuma an gano wani sikeli mai amfani da lantarki, da kuma ledojin saka kaya masu yawa da wata baƙar mota RAV 4 mai lamba Lagos KSF 872 GQ.

TRT Afrika