A ranar Laraba 12 ga watan Yuni, shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabi ga 'yan ƙasar, domin murnar zagayowar Ranar Dimokuraɗiyya ta wannan shekara.
Tun a mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ne aka sauya ranar bikin mulkin farar-hula a ƙasar, daga ranar 29 ga Mayu, wanda shi ne ranar da soji suka miƙa mulki ga farar-hula a shekarar 1999, zuwa 12 ga watan Yuni.
Ita dai ranar 12 ga Yuni, ita ce ranar da ta dace da ranar babban zaɓen shekarar 1993, wanda aka yi a ƙasar a zamanin mulkin soja na Shugaba Ibrahim Babangida, wanda gwamnatin sojin ta soke tun kafin a sanar da wanda ya lashe zaɓen.
Ga jerin abubuwa da Shugaba Tinubu ya taɓo, dangane da tarihin gwagwarmayar dimokuraɗiyya a Nijeriya, da wanzuwar mulkin farar-hula tsawon shekaru 25, da kuma ayyukan da gwamnatinsa take yi a yanzu.
1) Gwawarmayar dimokuraɗiyya
Shugaba Tinubu ya jinjina wa gwaraza maza da mata 'yan gwagwarmayar dimokuraɗiyya, da suka rasa rayukansu a fafutukar musamman CIf MKO Abiola, wanda ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Yunin shekarar 1993, da kuma mai ɗakinsa Hajiya Kudirat Abiola.
Shugaban ya kuma yaba wa sauran waɗanda suka sadaukar da rayukansu a gwagwarmayar, irinsu marigayi Janar Shehu Musa 'Yar Adua, da Pa Afred Rewane, Cif Anthony Enahoro, Dan Suleiman, Cif Chukwuemeka Ezeife, Gani Fawehinmi, da Cif Bola Ige.
Akwai kuma su Cif Olu Falae, Bolaji Akinyemi, Wole Soyinka, Femi Falana, Abdul Oroh, Cif Cornelius Adebayo, Olisa Agbakoba, da Sanata Shehu Sani, da kuma Gwamna Uba sani.
2) Tasirin 'yan jarida
Da yake yaba wa manyan gidajen jaridun da suka taimaka wajen kawo ƙarshen mulkin soji a Nijeriya, Shugaba Tinubu ya ce "Ba domin taimakon jajirtattun 'yan jaridun Nijeriya ba, da ba mu yi nasarar wannan yaƙin mayar da sojoji bariki ba."
'Yan jaridu masu rajin maido da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar sun fuskanci muzgunawa daga gwamnatocin soji masu mulkin kama-karya. An kame wasunsu an ɗaure su a gidan kaso.
Cikin manyan jaridun da suka yi yaƙi don tabbatar da damar faɗin albarkacin baki, da kawo dimokuraɗiyya, akwai jaridun National Concord, The Guardian, Punch, Tribune, The News/Tempo, da Tell.
3) Ƙalubalen tattalin arziki mai tsanani
Wani batu na da Shugaba Tinubu ya taɓo kuma shi ne na abin da ya kira "yaƙin bunƙasa tattalin Arzikin Najeriya". Shugaban ya amsa cewa ƙasar na fuskantar ƙalubalen tattalin arziƙi mai tsanani.
Ya ayyana cewa tattalin arzikin ƙasar na buƙatar garambawul, saboda cewa "an gina shi ne kan tubalin toka", sakamakon cewa yana dogaro kan kuɗaɗen shiga na man fetur kaɗai.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ɓullo da sabbin tsare-tsare don gina tattalin arzikin ƙasa, inda ya ce yana sane da cewa hakan zai iya haifar da raɗaɗi da matsi.
4) Sabon mafi ƙarancin albashi
Batun fitar da sabon mafi ƙarancin albashi, Shugaba Tinubu ya sanar da cewa ana ci gaba da tattauna da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar, "da zuciya ɗaya" don samun mafita da daidaito kan mafi ƙarancin albashi a ƙasar.
Shugaban ya ce nan ba da daɗewa ba za a aika da sabon tsarin zuwa Majalisar dokokin ƙasar, don sanya hannu kan matsayar da aka cim ma game da batun, inda ya ce dokar za ta yi aiki na tsawon shekaru biyar masu zuwa.
Ya kuma ce saɓanin yadda aka gani a wasu lokutan baya, gwamnatinsa ba ta tsangwami ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasar ba, yayin da suka kira yajin-aikin gama-gari, inda ya zaɓi hanyar neman fahimtar juna.
5) Inganta dimokuraɗiyya
Shugaba Tinubu ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su yi taka-tsantsan game da masu yunƙurin kawo cikas ga tsarin dimokuraɗiyyar da ƙasar take kai tsawon shekaru 25. Ya ce sahihin zaɓe shi ne turbar da ake gina dimokuraɗiyya mai ɗorewa.
Ya ƙara da cewa kyakkyawar dimokuraɗiyya tana inganta rayuwar al'umma ta hanyar samar musu da 'yanci, da haƙƙin yin tunani bisa raɗin-kansu, da rayuwa a inda suka zaɓa, da kuma yin abubuwan da suka so yi bisa doka.
A matsayinsa na wanda ya amfani da tsarin, shugaban ya sha alwashin kare dimokuraɗiyya, inda ya ce tsarin ba ya nufin samun daidaiton ra'ayi. Ya kuma jaddada cewa "Mun yi kyakkyawan zaɓi, kuma ya wajaba mu ci gaba kan wannan zaɓi".