Hoton wajen gidan shugaban Gabon na farko Leon Mba a Libreville. Hoto/Getty Images

Wasu manyan sojoji a kasar Gabon sun bayyana a gidan talabijin da sanyin safiyar Laraba inda suka sanar da kifar da gwamnatin kasar, sa’o’i kadan bayan ayyana Shugaba Ali Bongo Ondimba da hukumar zaben ta a matsayin wanda ya sake yin nasara a zaben kasar.

Ga abubuwa biyar da suka kamata ku sani game da Gabon:

'Yancin kan Gabon

Gabon kasa ce da ke yankin Tsakiyar Afirka, inda take da iyaka da Congo da Equatorial Guinea da kuma Kamaru.

Gabon ta samu 'yancin kai daga Faransa a ranar 17 ga watan Agustan 1960. Tun a shekarar 1882, Gabon ta kasance kasa wadda ke cikin French Congo a 1882 inda aka ware ta a matsayin kasa ta daban a 1906.

Kasar tana da girman kasa mai murabba'in kilomita 267,670 da kuma teku mai tsawon kilomita 885.

Iyalan Bongo

Iyalan Bongo ne suka kwashe fiye da shekara 55 suna mulki a kasar wadda ta samu ‘yancin kai daga Faransa a 1960.

Bongo, mai shekara 64, yana neman wa’adi na uku a zaben da aka gudanar ranar Asabar din da ta gabata, inda ya hau mulki a 2009, bayan rasuwar mahaifinsa Omar Bongo, wanda ya kwashe shekara 42 a kan mulki.

Mahaifin Bongo, wanda ya hau mulki a 1967, ya yi kaurin suna inda aka zarge shi da sace arzikin kasar – daya daga cikin mafi arzikin man fetur a duniya.

Bongo, mai shekara 64 ya nemi wa'adi na uku a zaben da aka gudanar ranar Asabar. Hoto/AFP

Dansa ya girma a matsayin dan-lelen mahaifinsa mai kudi, wanda yake mulkar kasar har ma ake masa take da ABO, Ali B.

A watan Oktoban 2018, Bongo ya sha fama da matsalar shanyewar rabin jiki inda ya yi wata goma yana fama. Hakan ne ya sa aka bayyana cewa bai cancanta ya ci gaba da mulki ba, inda a lokacin har aka yi yunkurin juyin mulki.

Kasa mai arzikin man fetur

Gabon na daga cikin kasashen da suka fi arziki a Afirka a ma'unin arzikin kasa idan aka kwatanta da yawan al'umma, inda take samun kudi mai dimbin yawa daga man fetur - yawan 'yan kasar miliyan 2.3 ne.

A shekarun 1970, kasar ta gano cewa tana da dumbin man fetur da ke cikin ruwa.

Kashi 60 cikin 100 na kudin shiga na kasar tana samunsa ne daga arzikin man fetur.

Sai dai kashi daya cikin uku na jama'ar kasar suna rayuwa a cikin matsanancin talauci, wato suna samun kasa da dala 5.50 a rana.

Kasar Afirka mai dazuka

Gandun-daji ne ya mamaye kaso 88 cikin 100 na kasar Gabon, lamarin da ya kasar ke da Gwaggon-birai da bauna da damisa da giwaye da sauransu.

Kasar tana daga cikin masu kira da a killace namun dawa, a yankin da ake fama da yake-yake da lalata dazuka da kuma sayar da namun dawa.

Gandun daji na Pongara wanda ke kusa da Libreville. Hoto/Reuters

A shekarar 2002, kasar ta kafa gandun dabbobi guda 13, wadanda suka rufe kaso 11 cikin 100 na kasar.

Daya daga cikin nasarar wannan mataki da aka samu ita ce killace giwayen Afirka da ke barazanar karewa.

Adadinsu ya ragu da kaso 86 cikin 100 a cikin shekaru 30 sai dai a Gabon sun ninka a cikin shekara 10.

Shahararren dan kwallon kafa

Dan wasan kwallon kafa na Gabon Pierre-Emerick Aubameyang wanda tsohon dan wasan gaban Chelsea ne, na daga cikin 'yan wasan gaba mafi iya taka leda a duniya.

Daga Borussia Dortmund ta Jamus wanda a nan ya yi suna, ya koma Arsenal a 2018 inda ya kasance daya daga cikin 'yan kwallon da suka fi cin kwallaye a Gasar Firimiya.

Sakamakon matakin da aka dauka na tsawatarwa, an tsige Aubameyang daga matsayinsa ne kyaftin din Arsenal inda daga baya ya bar Arsenal din baki daya ya koma Olympique de Marseille.

AFP