Shugaba Tinubu ya jagoranci zaman majalisar Ministocinsa a karon farko  a fadar shugaban kasar da ke Aso Rock: Shafin X/ fadar Aso Rock

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci sabbin ministocinsa su zage dantse don kawo sauye-sauye masu kyau ga rayuwar 'yan kasar.

Ya bayar da umarnin ne yayin taron majalisar zartarwarsa ta farko da ya jagoranta a ranar Litinin a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Taron ya mayar da hankali kan cimma muradun gwamnatin Tinubu don samar da hanyoyin ci-gaban tattalin arziki da wadata al'ummar Nijeriya da kuma kawo karshen talauci a kasar tare da jaddada muhimman ayyukan da ke gaban gwamnati.

Ga muhimman sharuda biyar da shugaban ya zayyana

1. Ba za a lamunci rashin kwazo ba: Shugaba Tinubu ya kafa wani tsari da zai sa ido wajen tabbatar da rikon amana da kuma tantance ayyukan da suka rataya a kan kowane minista.

Ya ce ba zai lamunci rashin kwazo daga wurin ministocin ba.

2. Sabon Tsarin Tattalin Arziki: Shugaban ya yi kira kan samar da sabbin dabarun bunkasa kasafin kudi na cikin gida da za su mayar da hankali wajen inganta rayuwar 'yan Nijeriya. '' Gwamnatin nan ta himmatu wajen sake farfado da harkokin kudadenmu na gida don walwalar 'yan Najeriya," a cewar Tinubu.

3. Ayyuka ba yawan lokacin mulki ba: Shugaba Tinubu ya jaddada cewa mukaman na ministocin ba nadi ne “yi-aiki-a-biya-ka” ba amma yana mai cewa ana auna mutuncin minista ne bisa irin ayyukan da ya yi wa kasa.

Labari mai alaka: 'Yan Nijeriya suna korafi kan yawan ministocin Shugaba Tinubu

4. Dabarun samar da tsaro da ci-gaban kasa: A kalaman shugaban, majalisar tana da alhakin aiwatar da manufofin da za su "gyara tattalin arzikin kasa tare da tabbatar da ci-gaban hadin kai da kuma karfafa tsaro don samar da zaman lafiya da wadata a Nijeriya."

5. Jagoranci mai sauki da karbar shawarwari: Shugaba Tinubu ya ce ya bude duk wata kofa ta karbar shawarwari don ciyar da gwamnatinsa gaba, yana mai tabbatar da cewa "a shirye nake na ba da hadin kai tare da sauraron jama'a."

Shugaban dai ya gargade ministocin da su yi kokari tare da ba da himma wajen cimma kashin farko na ajandar da gwamnatinsa ta sa a gaba guda takwas cikin shekaru uku da ke tafe.

Ya kuma bukaci su yi aiki tukuru domin farfado da tattalin arzikin kasar saboda Nijeriya na cikin mawuyacin hali.

TRT Afrika