Gwamnatin kasar Kongo Brazzaville ta musanta rahotannin da ake watsawa a soshiyal midiya cewa an yi yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Denis Sassou Nguesso ranar Lahadi.
Ministan Sadarwa na kasar Thierry Moungalla ya wallafa sako a shafinsa na X wanda a baya ake kira Twitter da ke cewa ya kamata ya yi “gaggawar” karyata rahotannin juyin mulkin domin kuwa na “kanzon-kurege”.
“Wasu bayanai na karya sun nuna cewa wasu manyan abubuwa suna faruwa a Brazzaville. Gwamnati tana musanta wannan labari na karya,” in ji shi.
“Muna masu tabbatar wa jama'a cewa komai na tafiya cikin kwanciyar hankali a (Kongo), kuma mutane na harkokinsu kamar yadda suka saba.”
Shugaban da ya yi shekara 38 a kan mulki
Tun da farko wasu rahotanni, da ba a san asalinsu ba, sun rika yawo a shafukan sada zumunta na X da Telegram inda ake zargin cewa “sojoji sun yi (yunkurin) juyin mulki a Kongo Brazzaville.”
Binciken da TRT Afrika ta yi a Brazzaville sun tabbatar da cewa babu wasu rahotanni na yamutsi a babban birni kasar ta Kongo.
Hasalima shugaba Nguesso ya isa birnin New York na Amurka ranar Lahadi domin halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 (UNGA).
Fargabar juyin mulki na karuwa a wasu kasashen Afirka tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar wanda ya kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yuli.
Kazalika sojoji sun hambarar da Shugaba Ali Bongo Ondimba na Gabon a karshen watan Agusta jim kadan bayan an sanar cewa shi ne ya sake lase zaben shugaban kasar karo na uku.