Ana sa ran tawagar za ta ja hankali sosai a wannan karon, sakamakon yanayin yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran.
Tawagar ta gudanar da atisayen ne a Belek, wani yankin shaƙatawa kusa da birnin Antalya da ke gaɓar tekun Medatareniya.
An takaita damar manema labarai sosai, inda jami'ai suka bayyana cewa suna son kauce wa duk wani abin da zai janye hankalin 'yanƙwallon kafin wasannin share fage masu zuwa, waɗanda aka bayyana a matsayin masu muhimmanci ga shirye-shiryensu.
A ƙarshen wannan mako Iran za ta buga wasanni biyu a Antalya, tsakaninta da Nijeriya da kuma Costa Rica. Jami'an tawagar sun bayyana cewa waɗannan wasannin jigo ne ga shirye-shiryensu na ƙarshe.
Asali an shirya gudanar da wasannin na sada zumunci ne a ƙasar Jordan, amma aka mayar da su Turkiyya biyo bayan ɓarkewar yaƙin Iran.
