Sannan akwai daya bangaren na wasu gungun mutane ko kungiyoyin asiri da ke tara mata a cibiyoyin da ake kira “baby factories” ko “child harvesting centers”
Wadannan miyagu suna sace ‘yanmata su yi garkuwa da su, ko su yaudare su don killace su da mayar da su kamar beraye, suna musu ciki ko fyade, suna ciyar da su har zuwa lokacin haihuwa, sannan su karbe jariran su kai kasuwannin bayanfage don neman riba.
Masana kiwon lafiya suna gargadin mata masu ba da hayar mahaifarsu ba bisa tsarin dokar lafiya ba, da su gujewa hakan saboda matsalolin lafiya.
A saurari karin haske daga cikin wannan shiri
