A cikin shekaru 20 da suka gabata, Turkiyya ta haɓaka alaƙarta da Afirka daga ƙarancin ayyukan diflomasiyya zuwa haɗin gwiwa daban-daban da ya ƙunshi cinikayya da ilimi da al'adu, da kuma tsaro.
Cinikayya da kasuwanci tsakanin ɓangarorin biyu ya wuce dala biliyan 40, dubban ɗaliban Afirka yanzu suna shiga jami'o'in Turkiyya, kuma wasannin kwaikwayo na talabijin na Turkiyya sun sami karɓuwa a faɗin nahiyar.
A cikin tsarin "Mafitar Afirka ga Matsalolin Afirka", Turkiyya ta samar da kadarorin soja waɗanda suka sauya sakamako a yankunan da ake fama da rikici don fifita halastattun gwamnatoci, wanda hakan ya sa haɗin gwiwar tsaro da Turkiyya ya zama abin jan hankali ga ƙasashen Afirka.
Masana sun ce ƙasar ta sanya kanta a matsayin mai shiga tsakani mai muhimmanci tsakanin tsarin tsaron Yamma da Nahiyar Afirka.
"Turkiyya ta gabatar da kanta ga abokan hulɗarta na Afirka a matsayin ƙasar Afro-Eurasia, ba ta Yammacin duniya ba, ba mai mulkin mallaka ba, amma tana da alaƙa da duniyoyi biyu," in ji Mursel Bayram, shugaban Cibiyar Nazarin Afirka a Jami'ar Kimiyyar Zamani ta Ankara, a tattaunawarsa da TRT Afrika.
"Wannan tsari yana da tasiri, ina ganin yana bai wa Ankara damar bai wa gwamnatocin Afirka damar samun fasahar soji ta NATO da ƙwarewar tsaro ba tare da ribar siyasa ba wanda a al'ada ake gani a haɗin gwiwa da ƙasashen Yamma.
"Don haka, lokacin da Ankara ta ce za ta iya isa ga NATO da Kudancin duniya, ba wai kawai da'awa ba ce, akwai wani abu tattare da hakan."
Maimakon tsaffin tsarukan tsaffin ƙasashe ‘yan mulkin mallaka - waɗanda suka haɗa da shiga tsakani kai-tsaye, kafa sansanonin dindindin da shigar sojoji ta ƙasa - shawarar Turkiyya ita ce gina ƙarfin kasa da sojojin gwamnati waɗanda za su iya aiki da kansu.
"Shawara ce ta daban daga abin da Faransa ta yi a yankin Sahel, inda sojojin gida galibi suka dogara da kayan aiki da tallafi na Faransa. Darasin a bayyane yake, ku bar ƙafarku ta zahiri ta zama ƙarama kuma ƙafarku ta fasaha ta zama babba," in ji Bayram.
Turkiyya ta kuma amince da yarjejeniyoyi na soja tare da ƙasashe kamar Nijeriya don sauƙaƙa musayar fasaha don ƙera kayan aikin soja.
Wasu kamfanonin Nijeriya sun riga sun yi hulɗa da kamfanonin tsaron Turkiyya don binciken haɗin gwiwar samar da kadarori don yaƙi da ƙungiyoyin ta'addanci kamar Boko Haram da reshenta mai alaƙa da Daesh da aka sani da ISWAP.
Manufar ita ce zama lafiya
Rundunar Sojin Turkiyya na gudanar da bayar da horo a wasu ƙasashen Afirka da dama a fannin yaƙi da ta'addanci da fasahar soja don haɓaka zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Manufar ita ce a bar waɗannan rundunonin su iya aiki da kansu.
"Ta hanyar horar da sojojin gida yadda ya kamata da kuma samar da kayan aikin kare kai, Turkiyya ta sanya kanta a matsayin mai ba da damar dogaro da kai ga Afirka maimakon mai ba da garantin tsaro daga waje," in ji Bayram.
"Wannan yana da alaƙa da abokan hulɗar Afirka ta hanyoyin da tsarin zaman lafiya na gargajiya na Yammacin duniya ba sa yi."
Misali, a Somalia, Turkiyya ta inganta tsarin rundunar sojojin Somalia, da ba su horo, da samar da kayayyakin more rayuwa na soja, da kuma kayan aiki.
Rundunar sojojin ruwa ta Turkiyya ta kuma samar da jiragen sama na horo na bincike da ceto ga Senegal a matsayin wani ɓangare na babban ƙoƙarinta na ƙarfafa haɗin gwiwar soja tsakanin ƙasashen biyu.
Turkiyya ta kuma ba da gudunmawar ma'aikata masu aiki ga Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu, da Mali, da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da Sudan da kuma Somalia.
"Turkiyya tana da ƙwarewa sosai a yankinta game da yaƙi da ayyukan 'yan ta'adda. Da wannan gogewa, Turkiyya za ta iya taimaka wa ƙasashen Afirka waɗanda ke fuskantar irin waɗannan ƙalubalen na tsaro," in ji Ahmet Kavas, tsohon Jakadan Turkiyya a Chadi da Senegal, a tattaunawarsa da TRT Afrika.
"Tun farkon shekarun 2020, ƙasashen Afirka da dama sun fuskanci waɗannan matsalolin kuma suna amfana daga gogewar Turkiyya, musamman ƙasashe kamar Habasha, da Sudan, da Somalia, da Mali, da Burkina Faso, da Jamhuriyar Niger da kuma Senegal."
Shugaba Recep Tayyip Erdogan, da farko a matsayin firaminista sannan kuma a matsayin shugaban ƙasa, ya kai ziyara sama da sau 50 a Afirka, wanda hakan ya sanya shi zama shugaban duniya da ya fi ziyartar nahiyar.
Kiransa na cewa "duniya ta fi biyar girma" ya kasance wani yunƙuri na yin gyare-gyare a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, da sauran abubuwa, don nuna ƙarfin Afirka a cikin tsarin ƙasashen duniya.
"Kiran yana ƙalubalantar tsarin duniya da ƙasashen Yamma ke mamaye komai kuma yana ba abokan hulɗar Afirka sauyi da ke fifita 'yancin kai, saurin habaka da inganta yanayin ciniki. Ina ganin gwamnatocin Afirka da yawa, na ganin hakan ya fi dacewa da su," in ji Bayram.
A ɓangaren tattalin arziki, Turkiyya ta bayar da wasu hanyoyin da za a bi don nahiyar da aka daɗe ana ɗaukarta a matsayin wurin gasa mai zafi ga albarkatun ƙasa tsakanin tsoffin ƙasashen mulkin mallaka da kuma ƙasashe masu tasowa.
Wannan na faruwa ne saboda sauyin yanayi a Afirka wanda ya sanya ƙasashen yamma ba sa jituwa da juna. Gwamnatocin Afirka suna ƙara yin tambaya game da yadda ƙasashen yamma ke tsoma baki a harkokin cikin gida da ikon mallaka tare da tunanin mulkin mallaka na zamani.
Ba ta mulkin mallaka
Tasirin da Turkiyya ke da shi a yankin kudu da hamadar Sahara yanzu ya haɗa da layin dogo mai tsawon kilomita 400 wanda ya haɗa Habasha da Djibouti da ke gabar teku, sansanin soja a Somalia, babban wurin wasanni na cikin gida a gabashin Afirka, wanda aka gina a Rwanda, da kuma tashoshin wutar lantarki masu yawo a kan teku waɗanda ke samar da wutar lantarki a Saliyo da Guinea-Bissau.
Duk da haka, alkaluman kawai ba su bayyana cikakken girman dangantakar da ke tasowa ba. Don share fagen haɗin gwiwar tattalin arziki, Turkiyya ta kulla yarjejeniyoyi na cinikayya da haɗin gwiwa a fannin tattalin arziki tare da ƙasashen Afirka 49.
Sauyin da aka samu a dangantakar Turkiyya da Afirka ya fara ne a shekarar 2005, lokacin da ta sami matsayin mai sa ido tare a Tarayyar Afirka, kuma Ankara ta ayyana ta a matsayin "Shekarar Afirka".
A cikin shekaru ashirin da suka gabata, kasancewar Turkiyya a fannin diflomasiyya ya faɗaɗa zuwa ofisoshin jakadanci 44 a nahiyar, yayin da kamfanin jirgin saman Turkiyya, Turkish Airlines, ke gudanar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa wurare 64 a cikin ƙasashen Afirka 42.
Ankara ta kuma karɓi baƙuncin shugabanni da dama, shugabannin gwamnati, da shugabannin kasuwanci don tattaunawa da ƙarfafa alaƙa.
Babban birnin Turkiyya ya kuma shaida sanya hannu kan yarjejeniyoyin kasuwanci, sulhu don kawo karshen rikici da kuma amincewa da yarjejeniyoyin da suka shafi tsaro.
"Babban bambancin ya ta'allaka ne da labarin da kuma tsarin aiki. Tsarin da tsoffin 'yan mulkin mallaka suka bi a Afirka yana da nauyi, son kai da kuma tilasta wa kasashen. Ko da kuwa manufofinsu a yau suna da kyau, wannan tarihin yana fayyace kowace hulɗa. Al'ummar Afirka suna jin hakan kuma shugabannin Afirka ba za su iya yin watsi da hakan ba," Bayram ya shaida wa TRT Afrika.
"Turkiyya ta zo ba tare da wannan gadon ba kuma ta yi niyya sosai game da gina wani sabon tsari na daban."









