Ma’aikatar Yaƙi ta Amurka, Pentagon, ta umarci kamfanonin kayan tsaro na ƙasar su hanzarta ƙera makamai tare da bayar da su a yayin da yaƙin Iran ya kusa ƙarar da muhimman makamai na Washington, a cewar wani rahoto na kafar watsa labarai.
Jaridar The Washington Post ta ruwaito cewa Mataimakin Sakataren Ma’aikatar Yaƙin ƙasar Steve Feinberg ya aike da wata wasiƙa ga shugabannin kamfanonin ƙera makamai a ranar Laraba inda ya ba su wa’adin kwana 21 su gabatar da shirinsu na “gaggauta ƙera makamai” domin yin aiki mai matuƙar muhimmanci.

"Ba za mu yarda a kwashe shekaru ana ƙera su ba," in ji Feinberg.
"Dole ne mu gaggauta shirinmu da kuma faɗaɗa ƙarfin samar da makamai a yanzu."
Wannan umarni yana zuwa ne a yayin da Pentagon take neman ƙara yawan makaman da ke rumbunta, cikinsu har da makaman da ke kakkaɓo makamai masu linzami samfurin Patriot da Terminal High Altitude Area Defense (THAAD).
Cibiyar Tsare-Tsare da Harkokin Ƙasa da Ƙasa ta ce an samu raguwar makamai masu linzami na Patriot daga 2,200 kafin soma yaƙin Iran zuwa 827, yayin da makamai samfurin THAAD suka raguwa daga 452 zuwa 278.
Ma’aikatar yaƙi ta Pentagon ta ce ta bayar da wa’adi ga manyan ‘yan kwangilar makamai da kamfanonin fasaha su faɗaɗa aikin samar da makamai.




















