Shin fasahar AI za ta iya zama barazana ga bil'adama? Ga abin da ke tattare da wannan muhawarar
KIMIYYA DA FASAHA
8 minti karatu
Shin fasahar AI za ta iya zama barazana ga bil'adama? Ga abin da ke tattare da wannan muhawararShugabannin kamfanonin AI suna gargaɗin cewa tsarin da ke ƙara samun ƙarfi zai iya haifar da manyan haɗɗura idan ci-gabansa ya zarce matakan tsaro.
Manhaojin AI za su iya karɓe iko da wnai sashi na intanet nan da shekara ɗaya, in ji shugaban kamfanin Anthropic CEO Dario Amodei. [Tsohon Hoto]

Sabbin gargaɗi daga masana'antar Ƙirƙirarriyar Basira sun sake farfaɗo da muhawara mai tsawo kan ko ingantacciyar fasahar Ƙirƙirarriyar Basira za ta iya tserewa daga ikon ɗan adam kuma a ƙarshe ta yi barazana ga rayuwar ɗan adam, da kuma ko kamfanonin da ke gina fasahar suna yin abin da ya dace don hana samuwar irin wannan yanayi.

Shugaban Kamfanin Anthropic, kamfanin San Francisco da ke bayan Claude, ya ce yana tunanin ya kamata masana'antar ta rage saurin aikinta, yana mai gargaɗi a ranar Asabar cewa tarin mahajoji na AI za su iya mamaye intanet cikin watanni shida zuwa shekara guda sai dai idan kamfanoni sun keɓe lokaci mai tsawo don samar da kariya.

Dario Amodei ya bayyana wani shiri ga kamfanoni kamar tasa da gwamnatoci a duk faɗin duniya don tabbatar da cewa samfuran AI masu ƙwarewa sun ci gaba da kasancewa daidai da umarni da dabi'un mutane masu sanin yakamata kwanaki bayan tsoffin masu bincike biyu na kamfanin AI na Anthropic sun bayyana damuwar cewa barazanar da AI za ta iya haifar wa ɗan Adam ba ta da yawa.

Ga abin da muka sani game da munanan hasashen da aka yi kwanan nan, da kuma ko za a iya dakatar da ci-gaban fasahar AI:

Manhajojin Ƙirƙirarriyar Basira na ƙra ƙarfi

Damuwa game barazana mai yiwuwa na fasahar suna ƙaruwa yayin da sabbin manhajoji na AI ke ƙara ƙarfi, lamarin da ke ƙara yiwuwar masu son aikata laifi su yi amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba kamar samar da cuta da kuma yaɗa cuta da kuma hatsari na manhajojin AI su kasance masu aikata laifuka a wata hanya mai hatsari.

Anthropic ta bayyana a makon da ya gabata cewa ta toshe kokarin da miyagun mutane ke yi na amfani da samfuran AI ɗinta don ayyukan mugunta, kamar hare-haren intanet da tattara bayanan sirri da bincike wanda ka iya haifar da makamai na ƙayoyin halitta.

Kamfanin ya ce ya sanya ƙarin kariya a cikin sabbin samfuransa don takaita binciken halittu waɗanda za a iya amfani da su don yin makamai amma ya lura cewa "yayin da samfuran ke ƙara zama masu iya aiki, haɗarinsu zai ƙaru, sai dai idan masu gina AI da masu kare al'umma sun yi aiki don tabbatar da cewa suna da ƙarin aminci."

A bara, Anthropic ta ba da rahoton cewa masu kutse sun yi amfani da AI na kamfanin a wani harin intanet da ke kai hari ga kamfanoni kusan 30 da hukumomin gwamnati a duk faɗin duniya.

Samfurin AI da yawa sun sarrafa kansu

Idan wani wakilin AI "ya zama mai aikata laifi," yana nufin AI ta ɗauki mataki fiye da aikin da aka umarce ta ta yi.

Anthropic da OpenAI, waɗanda suka ƙera ChatGPT, sun ce a watan Yuli samfuran AI ɗinsu sun yi nasarar yin aiki da kansu.

Anthropic ya bayyana cewa samfuran AI guda uku - Claude Opus 4.7, Claude Mythos 5 da kuma samfurin gwajin bincike na ciki - sun yi kutse cikin wasu ƙungiyoyi uku yayin gwaji kwanaki kaɗan bayan OpenAI ta bayyana cewa tsarin AI ɗinta ya yi kutse cikin sabar kamfanin fara AI Hugging Face.

OpenAI ta bayyan kutsen da wasu wakilan AI, ciki har da sabuwar manhajar GPT‑5.6 Sol da kuma wata “mai ƙrin ƙarfi” da ake kan gwadawa a cikin gida, a matsayin “muhimmiyar aba ta tsaro.”

Meta ma ta bi wannan hanyar a farkon watan Agusta da irin wannan batu inda wani wakilin AI ya kutsa ta tsaron intanet na wani kamfani.

Duk da cewa wasu masu sa ido sun lura cewa mutane sun cire wasu ababen kariya a OpenAI da Anthropic, waɗannan abubuwan sun bayyana a matsayin misalin ɗaya daga cikin manyan fargaba game da fasahar AI: cewa idan waɗannan tsare-tsare na kwamfuta suka kai matakin "Artificial General Intelligence" (AGI)—wato kalmar da ke bayyana fasahar AI mai ikon yin ayyukan tunani iri-iri daidai da ko ma fiye da yadda ɗan adam ke yi—to fasahar na iya haifar da mummunan bala'i da ba za a iya magance shi ba, ko kuma ta mallaki ɗan adam baki ɗaya

Yadda ko kuma lokacin da AI za ta iya haddasa bala’i abu ne da ake muhawar a kai

Yanayin bala’in da ake zayyanawa sun kashi kashi biyu ne: Wata AI da ta sami basirar inganta kanta mai sarrafa mutane maimakon mutane su sarrafa ta, ko kuma wata AI da wata “ƙasa mai laifi” ko kuma “masu aikata laifuka” ke juya ta.

Damuwa cewa ƙirƙirarriyar Basira za ta iya ɗara maƙurar ɗan Adam kan inda za ta iya kaiwa da matakan da za ta iya ɗaukawa ba sabbin abubuwa ba ne.

Alan Turing, wani masananin lissafin Birtaniya da ake gani a matsayinɗaya daga cikin waɗanda suka fi sani game da AI, ya yi hasashe a shekarar 1951 cewa AI za ta ƙarbe iko daga mutane.

Ƙasa da shekara goma bayan haka, Norbert Wiener, wani masanin lissafi, ya yi gargadin cewa na’urori masu basira za su yi kokarin cim ma nasu manufofin, kuma mutane ba za su iya dakatar da su ba.

A shekarar 2026, yayay ƙarfin hujja game da fargabar cewa fasahar AI—ko ta hanyar kubucewa daga ikon mutane ko kuma ta hanyar da wasu miyagun mutane za su yi amfani da ita ta hanyar da ba ta dace ba—za ta iya haifar da mummunan bala'i ko kuma rushewar al’ada da wayewar ɗan Adam?

Babu wnada ya sani

Masana a faɗin fannin kimiyyar kwamfuta da falsafa da sauran fannoni sun yi hasashen hanyoyi da dama da tsarin fasahar AI na gaba zai iya haifar da bala'i a duniya, ko dai ta hanyar kuɓucewa daga ikon ɗan Adam ko kuma a hannun mutane marasa tausayi.

Suna kamawa ne daga tura makamai da gano wani cuta mai kisa zuwa karkatar da gwamnatoci zuwa rikici ko wargaza hanyoyin sadarwa na abinci, makamashi da al'ummomin da ke dogaro da su.

Babu wani kiyasi da aka fi yarda da shi sosai game da lokaci mafi kusa da ɗaya daga cikin waɗannnan yanayin zai iya faruwa kua babu wata matsaya da aka cim ma game da yiwuwar aukuwar hakan.

A shekarar 2023, Cibiyar Tsaron AI mai zaman kanta ta fitar da wata sanarwa da masu bincike fire da 350 da shugabannin fasaha suka sanya wa hannu, ciki har da Amodei na Anthropic da kuma shugaban OpenAI Sam Altman, suna cewa: "Rage barazanar ƙarewar jinsi daga AI ya kamata ya zama abin da duniyata fi bai wa fifiko tare da annoba da yakin nukiliya."

Rahoton tsaron AI na shekarar 2026, da aka rubuta da shawarar fiye da masana masu zaman kansu 100, ya ce tsare-tsaren yanzu sun nuna lamau na farko-farko na wasu iko masu alaƙa amma ba a dukkkan matana da za su iya ba da yiwuwar rasa iko ba kuma ya bayyana hatsarin yiwuwar hakan da yanayin da lokaci a masatyin “abu da ke da wuyar ganewa da ba a saba gani ba.”

Wasu na jaddada buƙatar tsaron AI kafin lokaci ya ƙure

Wani mai bincike na Anthropic ya bayyana a makon da ya gabata cewa shi zai ajiye aiki da kamfanin game da damuwar cewa kamfanin ko abokan gogayyarsa ba sa ɗaukar matakan da suka dace wajen gina fasahar.

A saƙonnin da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Jacob Coxon ya yi ƙiyasin yiwuwa ta kashi 10 cikin 100 cewa AI za ta iya haddasa ƙarewar bil Adama cikin shekaru 10 masu zuwa kuma ya ce Anthropic da OpenAI “suna tsere zuwa matakin basira mai iya inganta kansa kuma suna caca da rayukanmu.”

Altman ya yi shelar cewa OpenAI ba za ta shiga kasuwar hannayen jari ba a shekarar 2026, inda yake ishara ga damuwa game da tsaroƙirƙirarriyar basira wanda ke yiwuwar ta kashi 10 cikin 100 ta cewa AI za ta iya haddasa ƙareway bil Adama ba da shekara goma a matsayin “abin da ba za a lamunta ba”.

asu bincike sun yi kira da a rage saurin gina AI kuma sun shafe shekaru suna gargaɗin cewa fasahar za ta iya haddasa barazana ga ci gaba da samuwar bil Adama.

Biyo bayan ababen da suka faru kwnanan nan, masana sun yi kira da a samu ingantaccen gwaji daga kamfanonin AI da ƙarin tattaunawa tsakanin Amurka da China domin sake fitowa da mafita ta tarayya.

Amma AI na girma sosai ta yadda gwamatoci da tsare-tsaren gwaji ke faman bibiyar fasahar. Ƙasashe na fitowa da dokokinsu, inda wasu ke cin karo da juna.

Shugaban China Xi Jinping ya yi gargaɗi a wani taro a watan Yuli game da buƙtar da ke akwai ta hana AI kuɓucewa daga ikon dan Adam.

Daga farko gwamnatin Shugaba Trump ya nuna jan-ƙafa wajen ƙaƙba doka kan AI, amma ya zama wanda ya fi mayar da hankali wajen rage hatsarun tsaron intanet .

A ranar Lahadi, Shugaba Trump ya yi ƙasa-ƙasa buƙatar da ke akwai ga gwamnatinsa ta taƙaita gina AI, amma ya yarda da buƙatar saka doka.