| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya za ta bayar da ƙarin ɗanyen mai ga matatar man Dangote a watan Mayu
Kamfanin man Nijeriya NNPC zai bayar da ɗanyen mai cikin jiragen ruwa bakwai a watan Mayu ga matatar man Dangote ta Nijeriya, maimakon jirage biyar da ake bai wa matatar a watannin da suka gabata.
Nijeriya za ta bayar da ƙarin ɗanyen mai ga matatar man Dangote a watan Mayu
Matatar man Dangote ta ƙara yawan man fetur da take sayar wa a kasuwar cikin Nijeriya. / Reuters / Reuters
4 awanni baya

Kamfanin man Nijeriya NNPC zai bayar da ɗanyen mai cikin jiragen ruwa bakwai a watan Mayu ga matatar man Dangote ta Nijeriya, maimakon jirage biyar da ake bai wa matatar a watannin da suka gabata, kamar yadda majiyoyi na ɓangarorin biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters.

Farashin mai a Nijeriya ya kai matakin da bai taɓa kaiwa ba a tarihi kuma matatar Dangote ta bayyana a baya cewa tana iya samun ɗanyen mai cikin jiragen ruwa biyar ne kawai a wata, lamarin da ya kasa sosai idan aka kwatanta da 13 zuwa 15 da take buƙata, abin da ke tilasta mata shigowa da sauran kan farashin da yaƙin da ake a Gabas ta Tsakiya ke ƙaƙabawa.

Masu AlakaTRT Afrika - Tashin farashin mai a Nijeriya ya yi ƙamari yayin da yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran ya ƙi ƙarewa

Ware ƙarin mai ga matatar man mai tace gangar mai 650,000 a ko wace rana, mafi girma a Afirka, zai kuma iya rage yawan ɗanyen man da Nijeriya da za a iya fitarwa a wannan lokaci da yaƙin Iran ya sa aka rage samun mai daga Gabas ta Tsakiya sosai, lamarin da ke tilasta wa masu sayen man su nemi ɗanyen mai cikin jiragen ruwa daga wurare masu nesa.

Matatar man Dangote ta ƙara yawan man fetur da take sayarwa a kasuwar cikin gida ta Nijeriya a cikin watan Maris, inda ta ke biyan buƙatar abin da ya ɗan ɗara kashi ɗaya cikin uku na litar mai miliyan 60 da Nijeriya ke buƙata a ko wace rana.

Kazalika matatar ta ƙara farashin man da kashi 13 cikin 100.

MAJIYA:reuters