| Hausa
TURKIYYA
3 minti karatu
Turkiyya ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyin da ƙimarsu ta kai $5.1B a taron COP31
Yarjejeniyoyi goma da bankuna huɗu na ƙsa da ƙasa za su tallafa wa matakai kan sauyin yanayi da kayayyaki masu jure bala'i da sabunta masan'antu tare da sauyin da ya dace da yanayi da na dijital.
Turkiyya ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyin da ƙimarsu ta kai $5.1B a taron COP31
(Tsohon Hoto) Yayin da yake magana a wani bikin rattaɓa hannu, Simsek ya ce za a gina zuba jarin kan tattalin arziki mai juriya da ya dace da muhalli / Anadolu Agency (Wire)

Turkiyya ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyi 10 da kimarsu ta kai dala biliyan $5.1 da bankuna ƙasa da ƙsa huɗu a wajen taron yanayi na COP31 a Antalya, kamar yadda ministan Kudi Mehmet Simsek ya bayyana ranar Alhamis.

Yarjejeniyoyin sun haɗa da Bankin Raya Asia (ADB) da Bankin Samar da Ababen More Rayuwa na Asia (AIIB) da Bankin Duniya da kuma Bankin Wanzar da Cigaba na Musulunci.

Da yake magana a wajen bikin rattaɓ hannu kan yarjejeniyoyin, Simsek ya ce samar da kuɗin zai taimaka wajen gina tattalin arziki da ya fi dacew ada yanayi da kuma ya fi juriyat hanyar ayyuka da ke tallafa wa samar da ayyukanyi da zamanantar da masana’antu da sauyin da ya dace da yanayi da dijital.

Turkiyya ta samu kimanin dala biliya $50 a msatyuin kuɗin aiki daga abokanan hulɗa na ci-gaba na waje tun shekarar 2023, in ji shi.

Kuɗin ya taimaka wa sake gini bayan girgizar ƙasa da layin dogo da kawar da amfanin da makamashin da ake haƙowa da samar da makamashin da ake iya sabuntawa da asibitoci masu juriya da masu fitar da kayayyaki da ƙananan masana’antu.

Simsek ya ce manufofin tattalin arziki masu kyau da gyara tsare-tsaren suna da muhimmanci ga janyo zuba jari na dogon zango, yana mai ƙarawa da cewa kasafin kudin ƙasashe kawai ba za su iya biyan buƙatun kuɗi na wannan sauyin ba.

ADB na tallafa wa asibitoci da ƙananan masan’antu

Shugaban ADB Masato Kanda ya ayyana yarjejeniyar Euro miliyan €620 (dala miliyan $687) domin gina asibitoci masu iya jure wa bala’i da ƙarfafa hidimar jinya da kuma hiras da likitoci.

Kazalika za a ware wani dala miliyan $500 ta bankin VakifBank domin faɗaɗa samar da kuɗi ga ƙananan masana’antu, musamman a lardunan da ba su ci gab ada sosai ba kuma girgizar ƙasa ta shafe su, tare da mata ‘yankasuwa.

Simsek ya ce yarjejeniyoyin za su kawo tallafin kuɗin ADB ga Turkiyya zuwa dala biliyan $3.1 .

AIIB da Bankin Duniya sun shelar ba da kuɗi

Shugabar Bankin Samar da Ababen More Rayuwa na Asia (AIIB) Zou Jiayi ta yi shelar samar da dala biliyan $1.9, ciki har da dala biliyan $1.6 na gaggauta matakin yanayi na Turkiyya da kuma ƙarin samar da kudi.

Sauran dala miliyan $300 ɗin za a ware shi ta bankin fitar da kayayyaki na Turkiyya domin tallafa wa sauya harkokin masan’antu zuwa wnada ya dace da muhalli da kuma juriya ga firgicin tattalin arziki.

Shugaban Bankin Duniya Ajay Banga ya ce yarjejeniyoyi uku da kimarsu ta kai dala biliyan $1.5 za su taimaka wa birane da fannin nom ada masana’antu, ban da ƙarin zuba jari mai zaman kansa da bankin ke son ya harhaɗa.

Ya ce abubuwan da bankin ke yi a Turkiyya sun kai dala biliyan $32, lamarin da ya sa ta ɗaya daga cikin ƙasashen da ta fi harka a duniya, da kuma nuna sauya tattalin arzikin ƙasa a cikin hulɗar da suke yi da ta zarce shekaru 75.