| Hausa
KIMIYYA DA FASAHA
2 minti karatu
An fara baje-kolin fasahar jiragen sama ta TEKNOFEST a Istanbul
Taron TEKNOFEST, daya daga manyan baje-kolin kayan sufurin sararin samaniya da fasaha na janyo hankalin ɗaruruwan maziyarta.
An fara baje-kolin fasahar jiragen sama ta TEKNOFEST a Istanbul
Baje-kolin na gabatar da kayayyakin tsaro musamman na sama ga mahalarta: / AA

A ranar Larabar nan ne aka bude taron fasahar ƙere-ƙeren kayan sufirin sararin samaniya na Turkiyya TEKNOFEST a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

Gidauniyar Fasaha ta Turkiyya (T3) da Ma'aikatar Masana'antu da Fasaha ta Turkiyya ne suka shirya taron na kwanaki biyar, wanda ke gudana filin jirgin saman Ataturk da ke Istanbul.

Tun shekarar 2018 ake gudanar da TEKNOFEST tare da goyan bayan hukumomin gwamnati da dama, abokan aiki daga kamfanoni masu zaman kansu, da jami'o'i.

TEKNOFEST yana alfahari da adadin sabbin nau'ikan gasar da ake sabunta wa kowace shekara, TEKNOFEST ya ƙunshi manyan bangarori 58 da ƙananan rukunai 137.

Mahalarta daga ko'ina cikin duniya suna iya bayyana ilimi da gogewarsu, suna samun ci gaba mai mahimmanci a fagen cigaban fasahar kere-kere.

Fasaha, shauki da tashi sama

TEKNOFEST zai ci gaba da marabtar maziyarta har zuwa ranar Lahadi, kuma ba kawai tare da gasar nuna fasaha ba, har ma tare da ɗimbin abubuwan ban mamaki.

Bikin na nuna tashi da jiragen sama da ke kayatarwa, baje-kolin kayayyaki da dama, kayan fasaha, kayan kasuwanci na fasaha, da ayyukan tukin jiragen sama da dalibai za su yi, inda ake tattara abubuwan fasaha da ban sha’awa a lokaci guda.

An saba gudanar da bikin a garuruwa daban-daban na Turkiyya dub bayan shekaru biyu, inda a Istanbul kuma duk bayan shekaru uku.

An kuma gudanar da bikin a kasashen waje guda biyu: Azerbaijan da Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus.

A watan da ya gabata an gudanar da Blue Homeland, wani bangare na TEKNOFEST a Istanbul.

Bikin da aka gudanar a shekarar da ta gabata a birnin Adana na kudancin Turkiyya, TEKNOFEST ya ja hankalin maziyarta kusan miliyan 1.1, wanda ya zuwa yanzu kusan miliyan 11 ne suka halarta.

Rumbun Labarai
Gidauniyar Gate da OpenAI sun ƙaddamar da shirin inganta lafiya ta hanyar fasahar AI a Afirka
Ɗan sama jannatin da ya kamu da rashin lafiya ya sa dole jirgin NASA ya dawo duniya
Duniyar dijital: Yadda annobar son waya da komfuta ke hana yara jin daɗin ƙuruciya da samun kulawa
Jirgin sama jannati mai zagaye sararin samaniya na farko da aka ƙera a Turkiyya zai fara aiki
Butum-butumin NASA ya ɗauki yadda aka yi walƙiya a duniyar Mars a lamarin da ba a taɓa gani ba
Masanin kimiyya na Turkiyya ya jagoranci 'yan sama jannati wajen gano sabbin duniyoyi
Hatsarin da ke tattare da gem din Roblox ga yara ya sa Saudiyya da UAE haramta shi
Hirar Xi da Putin kan tsawon rayuwa har shekara 150: Shin ilimin kimiyya ya kai wannan matakin?
An kai Agushi sararin samaniya ya yi kwana bakwai don yin binciken kimiyya a kansa
Afirka za ta iya zama 'kan gaba a fannin sabunta makamashi': Sakatare Janar na MDD
Iyakar ikon kasashe kan Kirkirarriyar Basira da abin da hakan ke nufi ga tsarin tafiyar da duniya
Grok ta dawo aiki bayan dakatar da ita don bankaɗar da ta yi kan kisan ƙare dangi na Gaza
Kirkirarriyar Basira na ƙoƙarin magana da harsunan Afirka, Ko ƙarshen watsi da harsunan ya zo?
WhatsApp ya rufe shafuka fiye da miliyan 6.8 masu alaƙa da zamba: Meta
Google ya amince tsarin gargaɗinsa ya gaza ceton miliyoyin mutane a girgizar ƙasar Turkiyya a 2023
Masana kimiyya sun ɗauki hoton da ba a saba gani ba na mutuwar taurari a kaunu
Amurka ta sauya wa kayayyakin sojinta wuri, ta rage shiga sansaninta mafi girma a Gabas ta Tsakiya
Meta na tattaunawa da kamfanin Scale AI domin zuba jarin fiye da dala biliyan 10 — rahoto
Masu fafutuka suna son a sauya tsarin TikTok saboda gazawar shafin daga kare yara
Ɓoyayyun duwatsun astiriyod na duniyar Venus za su iya faɗowa duniyarmu - Bincike