Hukuncin ba-zata na karɓe wa Senegal kambin Gasar Kofin Nahiyar Afirka (AFCON), tare da miƙa shi ga ƙasar da ta sha kaye, Maroko, ya shafi batutuwa fiye da na tantance wanda ya lashe gasar.
Batun ya bar matsayin babbar gasar ta Afirka a cikin ruɗani kuma ya ƙara nuna tsananin damuwa kan tsarin gudanarwa, da zargin tsoma baki daga waje a Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF), a cewar tsoffin 'yanwasa na ƙasa, da masu sharhi kan ƙwallon ƙafa a nahiyar.
Sharhi mafi kaushi ya fito a wannan makon daga tsohon ɗanwasan Afirka kuma Gwarzon Ƙwallon Duniya na Shekara, George Weah, wanda ya ce hukuncin “ya saka tabo a ƙwallon ƙafa na Afirka, kuma ya rage aminci da adalci, daidaito da gaskiya a wasanni a nahiyar,” a cewar wata sanarwa.
A wasan ƙarshe na AFCON a ranar 18 ga Janairu a babban birnin Maroko, Rabat, an ga 'yanwasan Senegal suna barin filin wasa don nuna adawa da hukuncin bai wa masu masaukin baƙi bugun fenareti a ƙarshen zagaye na biyu. Bayan 'yanwasan Senegal sun dawo fili a ƙarshe, Maroko ta ɓarar da fenareti, sannan Pape Gueye ya ci ƙwallo a ƙarin lokaci wanda ya bai wa ƙasarsa nasara da ci 1-0.
Amma Kwamitin Ɗaukaka Ƙara na CAF daga baya ya soke sakamakon, ya ba da kambin ga Maroko, yana nuna cewa ya yi hakan ne saboda halayyar tawagar Senegal.
'Kafa misalin da zai kawo matsala'
‘‘Hukuncin CAF ana iya kare shi a doka amma a zahirinsa yana da illa. CAF ta yi aiki cikin iyakokin ƙa'idojinta. Barin filin wasa da Senegal suka yi, ko da na ƙanƙanin lokaci ne, ya janyo tilas su haƙura da wasan bisa ƙa'ida,’’ in ji Tebogo Mokubung, masani kan ƙwallon ƙafa daga Afirka ta Kudu, a hira da TRT Afrika.
Ya ƙara da cewa, ‘‘Duk da haka, soke wasan ƙarshe da aka riga aka kammala yana raunana kalamai kan gaskiya a ƙwallon ƙafa kuma yana kafa misali mai cike da matsala domin ba a taɓa ganin irin wannan ba”.
An yi murna da wannan hukuncin a Maroko, inda mutane suka ɗauki abin a matsayin cewa an gyara wani rashin adalci na wasanni.
Amma Senegal ta sha alwashi kuma ta shigar da ƙara a Kotun Warware Jayayyar Wasanni (CAS), wadda ita ce kotun ƙarshe kuma mai zaman-kanta wajen warware rikice-rikicen wasanni. Kasar ta Yammacin Afirka ta kuma nemi a yi 'bincike mai zaman kansa na ƙasa-da-ƙasa kan zargin cin hanci da rashawa a hukumar gudanarwa ta CAF'.
‘Yanzu muna dogaro da tsarin warware jayayya na waje don taimaka mana wajen gudanar da wasanmu, kuma hakan na jefa shakku kan matakan gudanarwa a CAF,’’ in ji Mokubung.
'Runto a ƙwallon ƙafa'
Ga Weah, wanda ya taɓa shugabantar Liberia, ya ce bisa dokokin wasa, ya kamata a yanke hukuncinsa a fili kuma alƙalai su mallaki dukkan ikon yanke hukunci yayin wasa, amma a yanzu ana kassara tsarin ta hanyar sabon hukunci daga baya.
‘‘Ina kira ga Kotun Warware Jayayyar Wasanni da sauran hukumomin da abin ya shafa su ɗauki mataki cikin sauri domin wannan runton kada ya ɗore,’’ in ji shi.
Tsohon kyaftin ɗin tawagar Nijeriya, William Troost-Ekong, wanda ya kai ƙasarsa zuwa wasan ƙarshe na AFCON 2024, ya ce da shi ne a matsayin ɗanwasan Maroko, zai ƙi karɓar kofin da aka bayar a irin wannan yanayin.
‘‘Wani lokaci mutane suna jiran irin wannan abu ya faru don su yi dariya ga ƙwallon ƙafa a Afirka,’’ in ji shi, kamar yadda mujallar wasanni ta The Athletic ta ruwaito.
'Abin yi wa dariya'
Ƙwallon ƙafa shi ne wasa mafi shahara a Afirka, kuma masu sharhi suna tsoron cewa hukuncin CAF na iya kafa mummunan misali musamman a gasannin cikin gida, da sauran gasannin nahiyoyi.
‘‘CAF ta yi kuskuren hukunci, kowane hukunci Kotun Warware Jayayyar Wasanni ta yanke. Mu (Afirka) yanzu mun zama abin dariya. Wannan hukunci da ba a taɓa ganin irinsa ba ya nuna giɓin gudanarwa a ƙwallon ƙafa na Afirka,’’ in ji marubucin wasanni daga Kenya, Charles Nyende.
Wasu magoya bayan sun yi tsokaci kan yadda aka kai ga wannan hukunci mai rikici da kuma tsawon lokacin da aka ɗauka.
‘‘Wannan wata tuhuma ce kan ƙwallon ƙafarmu a Afirka ko kan yadda ake tafiyar da CAF. Babu yadda Senegal za ta iya lashe wasa ranar wasa sannan a dakatar da nasararta a baya, don ba wa Maroko kambin watanni biyu bayan kammala wasa. Ba shi da ma'ana domin wannan ba ƙwallon ƙafa ba ne,’’ in ji Roy Ogot a hira da TRT Afrika a babban birnin Kenya, Nairobi.
Rigimar ta kuma sanya shugaban CAF, Patrice Motsepe cikin kallon tuhuma, musamman bayan ya sake lashe zaɓe a bara tare da alƙawarin sanya AFCON cikin ɗaya daga cikin manyan gasannin wasanni a duniya, da inganta ƙa'idojin hukuncin alƙalai a nahiyar.
Motsepe ya shiga tsaka-mai-wuya
Motsepe ya samu nasarar janyo masu ɗaukar nauyi da masu watsa shirye-shirye na ƙasashen waje, amma masana suna gargaɗin cewa waɗannan ƙoƙarin na iya tarwatsewa saboda hukuncin da aka yanke a kan sakamakon wasan ƙarshe na AFCON.
‘‘A ƙarshe shugaban hukumar ana kallon sa a matsayin wanda ke ɗaukar nauyin lissafe-lissafen hukumar, ma'ana idan wani abu ya faru ba daidai ba, shi ke ɗaukar alhaki,’’ in ji Mokubung.
Ya kammala da cewa, ‘‘Wannan zai jefa shakku kan aikin da ya yi dangane da ko yana da ikon kan abin da ke faruwa a CAF. Domin a ƙarshe, kana buƙatar samun amincewa da nuna wa al'ummar ƙwallon ƙafa ta duniya cewa kai shugaban ƙwallon ƙafa na Afirka kana riƙe da ragama”.












