| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Trump ya dakatar da hari kan tashoshin makamashin Iran na kwana 10, ya ce ana 'ci gaba' da tuntuɓa
Trump ya yaba wa ci-gaba da aka samu kan tattaunawa duk da cewa Iran ta yi watsi da sharuɗɗan kawo ƙarshen yaƙin a matsayin wani abu 'da ya karkata ɓangare ɗaya kuma mara adalci'.
Trump ya dakatar da hari kan tashoshin makamashin Iran na kwana 10, ya ce ana 'ci gaba' da tuntuɓa
Trump ya ba da shawarar cewar Iran ta ƙyale tankokin mai 10 su wuce ta mashigin ruwan Hormuz a wata alama ta niyya mai kyau a tattaunawa. / AFP / AFP
27 Maris 2026

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi shelar cewa zai dakatar da hare-hare kan tashoshin makamashin Iran na kwanaki 10 kamar yadda Tehran ta nemi a yi kuma tattaunawa da Iran na ci gaba "da kyau," duk da cewa wani jami’in Iran ya yi watsi da sharuɗɗan Amurka na kawo ƙarshen yaƙin a matsayin "abin da ya karkata ɓangare ɗaya kuma mara adalci."

Yaƙin ya kashe dubban mutane, ya shiga ƙasashe maƙwabta kuma ya shafi tattalin arzikin duniya inda farashin makamashi ke ci gaba da tashi tun lokacin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da hare-hare kan Iran ranar 28 ga watan Fabrairu.

A ranar Alhamis, Trump ya yi barazanar ƙara matsin lamba kan Iran idan ba ta ƙulla yarjejeniya ba yayin wani taron ministoci a Fadar White House, amma daga baya ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa zai dakatar da hare-hare kan tashoshin makamashin Iran na kwanaki 10 zuwa ranar 6 ga watan Afrilu na shekarar 2026 (da misalin ƙarfe sha biyu na dare agogon GMT da safiyar 7 ga watan Afrilu).

Masu AlakaTRT Afrika - Damuwar 'yan Republican na ƙaruwa gabanin zaɓukan rabin wa'adi saboda tasirin yaƙin Iran

"Tattaunawa na ci gaba kuma, duk da kalamai na kuskure da suka saɓa wa hakan na kafafen watsa labarai masu labaran ƙarya, da kuma sauransu, suna tafiya yadda ya kamata," kamar yadda ya ƙara bayyanawa a saƙon da ya wallafa a shafin sada zumuntansa na Truth Social.

Daga baya ya shaida wa shirin “The Five” na kafar Fox News' cewa Iraniyawa sun nemi dakatar da yaƙi na kwanaki bakwai. Babu martani nan-take daga Tehran.

Iran ba ta nemi a dakatar da hare-hare kan tashoshin makamashinta na kwanaki 10 ba, kamar yadda jaridar Wall Street Journal ta ambato masu shiga tsakani a tattaunawar sulhun suna cewa.