Yadda yakin Gabas ta Tsakiya zai shafi ƙasashen Afirka a gajeren lokaci, in ji wani rahoto
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Yadda yakin Gabas ta Tsakiya zai shafi ƙasashen Afirka a gajeren lokaci, in ji wani rahotoƘasashen Afirka na fuskantar barazanar raguwar haɓakar tattalin arziki a bana idan yaƙin Gabas ta Tsakiya ya ci gaba, tare da kawo cikas ga kasuwanci na dogon lokaci, sannan jigilar makamashi da takin zamani na barazanar nakasa nahiyar.
kawo cikas ga zirga-zirga a mashigar Hormuz ya bakin tasiri kan kai mai nahiyar Afirka. / Reuters / Reuters

Ƙasashen Afirka na fuskantar barazanar raguwar haɓakar tattalin arziki a wannan shekarar idan yaƙin Gabas ta Tsakiya ya ci gaba, tare da kawo cikas ga kasuwanci na dogon lokaci, sannan jigilar makamashi da takin zamani na barazanar nakasa nahiyar, in ji wani rahoto da aka fitar a ranar Alhamis.

Rahoton da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya guda biyu, Tarayyar Afirka da Bankin Raya Afirka suka fitar ya ce tattalin arzikin Afirka zai iya raguwa da maki 0.2 a ma’ainin GDP a shekarar 2026 idan rikicin ya wuce watanni shida.

"Gwargwadon yadda rikicin da kuma yadda aka samu cikas a hanyoyin jigilar kayayyaki da samar da makamashi da takin zamani suka tsananta, to gwagwardon yadda barazanar raguwar ci-gaba a faɗin nahiyar zai karu," in ji rahoton, wanda aka gabatar da shi a taron Kwamitin Tattalin Arziki na Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a garin Tangier.

Rahoton bai auna tasirin da ka iya yi wa hauhawar farashin kayayyaki ba, amma ya yi gargaɗin cewa rikicin zai iya rikieɗwa cikin sauri zuwa matsalar tsadar rayuwa a faɗin Afirka ta hanyar hauhawar farashin mai da abinci.

Ya ce wasu ƙasashen Afirka za su iya fuskantar matsala sakamakon ƙarancin takin zamani fiye da hauhawar farashin mai.

Gabas ta Tsakiya na bayar da makamashi mai yawa ga Afirka

"Katsewar samun iskar gas samfurin LNG a yankin Gulf zai shafi samar da sinadarin ammonia da urea, wanda hakan zai ƙara farashin takin zamani da kuma takaita samar da shi a muhimmin lokacin shuka daga Maris zuwa Mayu," in ji rahoton.

Rahoton ya lura cewa Gabas ta Tsakiya ce ke samar da kashi 15.8% na kayayyakin da ake shigowa da su Afirka da kuma kashi 10.9% na kayayyakin da ake fitarwa daga nahiyar.

An ce, "ƙasashe kalilan," kamar Najeriya mai samar da mai da kuma fitar da iskar gas daga Mozambique, za su amfana da hauhawar farashin.

A cewar rahoton, sake fasalin sufuri ya riga ya ƙara yawan zirga-zirgar ababen hawa ta tashar jiragen ruwa ta Maputo da ke Mozambique, Durban da ke Afirka ta Kudu, Walvis Bay da ke Namibia, da kuma Mauritius.

Matattar jigilar kayayyaki

"A Gabashin Afirka, Kenya ta zama cibiyar jigilar kayayyaki ta hanyar Tashar Jiragen Ruwa ta Lamu da Nairobi, yayin da Habasha ke cin gajiyar rawar da take takawa a matsayin gadar jiragen sama ta gaggawa da ke haɗa Asiya, Afirka, da Turai ta hanyar Kamfanin Jiragen Sama na Ethiopea," in ji shi.

Rahoton ya ƙara da yin kira ga gwamnatocin Afirka da su ƙarfafa tattara kuɗaɗen shiga na cikin gida, daidaita sayo mai da kuma kafa hanyoyin samar da abinci na gaggawa, yayin da suke adana kudaden shiga daga man fetur da kuma aiwatar da matakan kare zamantakewa da ake da manufa a kansu.

Claver Gatete, Babban Sakataren Hukumar Tattalin Arziki ta Majalisar Dinkin Duniya kan Afirka, wanda ya rubuta rahoton, ya shaida wa manema labarai cewa ya yi wuri a tantance tasirin yaƙin kan hauhawar farashin kaya da ci-gaban Afirka, ko kuma a tantance ƙasashe da sassan da rikicin zai fi shafa a yanzu.


Rumbun Labarai
Mene ne Tehran ke gabatarwa domin kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran?
Araghchi ya faɗaɗa zirga-zirgar diflomasiyyar Iran daga Islamabad zuwa Moscow
Sisi na Masar ya yi gargaɗi kan 'ƙoƙarin da ake yi da gangan' na sake zana taswirar Gabas ta Tsakiya
Falasɗinawa na kaɗa ƙuri'a a zaɓen farko tun bayan yaƙin ƙare-dangi da Isra'ila ta ƙaddamar a Gaza
Iran ta ce ba kai-tsaye za a yi tattaunawa a Pakistan don kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra’ila ba
Turkiyya da ƙasashe bakwai sun soki Isra'ila kan keta alfarmar Masallacin Ƙudus
Trump ya fasa kai wa Iran hari da makamin nukiliya
Daraktan IEA ya ce ana asarar gangar mai miliyan 13 kullum saboda rufe Mashigar Hormuz
Amurka ta dakatar da jigilar dala zuwa Iraƙi, amma me ya sa take aika kuɗi zuwa Baghdad?
Trump ya tsawaita tsagaita wutar Iran domin bai wa Tehran ƙarin lokaci na tattaunawa
Vance zai tafi Pakistan ranar Talata domin tattaunawa da Iran  — rahoto
Sojan Isra’ila na shan suka bayan ya lalata mutum-mutumin Yesu a Lebanon
Iran ta kai harin ramuwar gayya kan jiragen Amurka a kan ƙwace jirgin dako: Rahoto
Isra'ilawa da dama sun mamaye Masallacin Ƙudus a ƙarƙashin rakiya da tsaron 'yansanda mai tsanani
Trump ya ce Amurka na yin tattaunawa mai kyau da Iran, ya yi gargaɗi kan rufe Mashigar Hormuz
Hare-haren Iran sun lalata fiye da gidaje 1,000 tare da mayar da su kufai a Tel Aviv - Magajin Gari
Iran ta kama mutum 127 kan zargin taya abokan gaba shirya kai mata hari ta ƙasa
Trump ya ce za a yi amfani da ‘manyan katafilolin tone kasa’ don kwashe sinadarin Uranium daga Iran
Iran ta sanar da bude Mashigar Ruwa ta Hormuz ga dukkan jiragen ruwan duniya
Jakadan Iran a MDD ya bayyana ƙawanyar Amurka a matsayin 'matakin tsangwama'