Yadda waya da soshiyal midiya ke lalata ƙwaƙwalwar yara
RAYUWA
5 minti karatu
Yadda waya da soshiyal midiya ke lalata ƙwaƙwalwar yaraNa san kuna kallon wannan bidiyo daga shafin  Facebook ne, ko Instagram ko kuma Tiktok a wayar da ke hannunku.
Binciken ya nuna cewa kashi 64.5 cikin 100 na wadanda aka tattauna da su suna goyon bayan sanya mafi karancin shekarun amfani da soshal midiya / AP



Amma kun san irin mummunar illar da wadannan shafuka suke yi wa kwakwalwar yara musamman ’yankasa da shekara 16?

To kada ku ji da wai, waya da kuma shafukan sada zumunta suna lalata kwakwalwar matasa da ’yanmata musamman idan ba a kayyade lokacin da za su rika amfani da su ba.

Shi ya sa kasashe kamar Australia, Malaysia, Brazil kuma Indonesia suka yi dokar da ta hana yara ’yankasa da shekara 16 shiga shafukan sada zumunta. Sai Turkiyya da Faransa da su kuma suka haramta wa yara ’yankasa da shekara 15 amfani da wadannan shafuka masu sace hankalin mai amfani da su.

Masana dabi’un dan’adam da likitocin kwakwalwa na wannan zamani suna yawan gargadi kan yawan amfani da soshiyal midiya da wayar salula, inda suke cewa suna haddasa ‘Gagarumin Sauyi a Tsarin Kwakwalwar Yara’ wato abin da suka yi wa lakabi da (The Great Rewiring) a Turancin Ingilishi.

Cikin illolin da hakan ke jawowa har da tarwatsa hankalin yara da kasa yin rayuwa ba tare da waya ba (wato addiction) da rage yawan barcinsu da hana su yin hulda da jama’a a zahiri.

Matsalar ba ta tsaya a nan ba, saboda wadannan matsalolin da na lissafa su kuma suna haddasa wasu sabbin manyan matsaloli kamar jawo wa yara koma baya a karatunsu da matsalolin kwakwalwa wato (mental health illness) a wasu lokuta ma hakan na sanya wasu yaran su kashe kansu bayan sun fada cikin tsananin damuwa (depression).

Na san iyaye da dama suna ganin wasu daga cikin wadannan alamomi musamman batun raguwa ta fuskar kokarin yara a makaranta, bayan yaran sun kwashe wani lokaci mai tsawo suna amfani da wayar salula da kuma shafukan sada zumunta.

Wani bincike da Ma’aikatar Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arziki na Zamani ta Nijeria ta gudanar a baya-bayan nan ya bayyana cewa fiye da ’yan Nijeriya kaso 80 cikin 100 da aka tattauna da su, suna goyon bayan kafa wasu dokoki na takaita amfani da kafofin sadarwa na zamani ga yara ’yankasa da shekara 16.

Binciken ya nuna cewa kashi 64.5 cikin 100 na wadanda aka tattauna da su suna goyon bayan sanya mafi karancin shekarun amfani da soshal midiya ya zama shekaru 16 ko 17, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya bayyana a farkon makon jiya.

Kazalika binciken ya nuna cewa manyan haduran da yara ’yan Nijeriya ke fuskanta a intanet sun hada da kallon abubuwa masu cutarwa ko wadanda ba su dace ba, sai kuma nishadin intanet da ke juyawa zuwa jaraba (addiction), da kuma masu yaudarar yara ta intanet da niyyar lalata tarbiyyarsu.

Duk da cewa wannan bincike ya bayar da shawarar kafa dokoki cikin gaggawa kamar yadda aka yi a kasashen Turkiyya da Faransa da Indonesia, masana suna bayar da shawarar cewa iyaye da malamai da shugabannin makarantu za su iya hada kansu don ceto yaran da suke karkashin kulawarsu daga wannan matsala.

Yayin da kafofin sadarwa na zamani ke samar da damarmaki na koyo da kirkire-kirkire da nishadi, masana na cewa ya zama wajibi a kare yara daga abubuwa masu cutarwa da ke cikin waya da soshal midiya, musamman saboda hakan yana rage kaifin basirarsu.

Masani kan dabi’un dan adam, Jonathan Haidt, wanda ya rubuta wani sabon littafi kan illolin waya da soshiyal midiya ga yara, mai suna: “The Anxious Generation” How the Great Rewiring of Childhood Is Causing an Epidemic of Mental Illness. A ciki marubucin ya bayar da shawarwari guda uku wadanda ya ce, idan iyaye, makarantu, da gwamnatoci suka hada kai suka aiwatar da su, za a iya ceto kwakwalwar matasa.

Ga muhimman shawarwarin da ya bayar:

1. Hana yara wayoyin salula na zamani (Smartphones) kafin su kai shekara 14

Abin da yake nufi: Kada a sayawa yaro ko yarinya wayar da ke da intanet da apps kafin ya shiga sakandare.
Madadin haka: Idan ana son a rika magana da yaro, a saya masa karamar waya mai tocila, wacce ba ta da intanet, sai dai kira da tura sako kawai.

2. Hana amfani da soshiyal midiya, sai yaro ya kai shekara 16

Abin da wannan ke nufi: Kamfanonin soshiyal midiya (kamar TikTok, Instagram, Facebook) kada su bar yara ’yankasa da shekara 16 su bude account. Saboda tilasta wa wadannan kamfanonin daukar wannan mataki ne ya sa kasashe irin su Australia, Turkiyya, da Faransa suka yi dokokin da muka tattauna a baya.

3. Hana wayar salula kwata-kwata a makarantu, Jonathan Haidt ya ce ya kamata makarantu su haramta wa dalibai amfani da waya tun daga safe har zuwa lokacin da za su tashi makaranta.

Ta wacce hanya makarantun za su tabbatar da hakan? Fitaccen marubucin ya bayar da shawarar cewa dalibai za su rika ajiye wayoyinsu a cikin wani akwati ko jaka ta musamman da safe idan sun zo makaranta,  sannan idan lokacin tashi ya yi, sai su dauki wayarsu, kuma za su iya kiran iyayensu, idan bukatar hakan ta taso bayan an tashi daga makarantar.