Uwar ‘ya’ya ‘yan-tara da su kaɗai ne aka taɓa haihuwarsu kuma suka rayu, ta sanar da cewa yaran za su shiga “wani muhimmin mataki” a rayuwarsu, yayin da suke shirin fara makaranta.
Yaran da suka haɗa da mata biyar da maza huɗu, sun cika shekara biyar a duniya a wannan mako, tare da iyayensu a ƙasar Mali, wato Halima Cisse da Abdelkader Arby, da yayarsu Arby, ‘yan shekara bakwai.
“Yaran suna cikin ƙoshin lafiya, Alhamdulillah. Lafiyayyu ne, masu kuzari, kuma cike da farin ciki. Suna ci gaba da girma cikin kyawu, kuma muna matukar godiya,” uwar su Halima Cissé ta gaya wa shafin Guiness World Records.
Ta ƙara da cewa, “Za su fara makaranta nan ba da jimawa ba, wanda yake muhimmi abu kuma mai ƙayatarwa a gare su. A matsayin iyaye, muna mai da hankali kan iliminsu yayin da muke tabbatar da sun ci gaba da jin daɗin zaman yarintarsu. Wannan sabon mataki wani babban canji ne ga iyalinmu.”
Haihuwarsu abin al'ajabi ne na likitanci, wanda ya jawo hankalin duniya bayan an haife su gabanin lokacin da ake tsammani, wato a mako na 30, ta hanyar tiyata a birnin Casablanca na Maroko.
Kowane jariri cikin yaran ya kasance yana da nauyin tsakanin kilogiram 0.5–1. Sun yi watanni tara na farko a Maroko, inda aka haife su, kafin a mayar da su Mali.
An sanya wa 'yan mata sunaye Kadidia, Fatouma, Hawa, Adama da Oumou, yayin da 'yan mazan suka sami sunayen Mohammed, Oumar, Elhadji da Bah.
Iyalin yaran sun yaɗa hotunan bikin ranar haihuwar, wani muhimmin mataki a rayuwarsu wadda ta samu soyayya da yabo daga mutane da dama.
“Yaran suna rayuwa tare da juna, da kuma 'yar uwarsu babba. Sun haɗa zumunci mai ƙarfi kuma suna cin da yawancin lokacinsu suna wasa tare. Kamar sauran ’yan-uwa, wani lokaci suna samun ƙananan saɓani, amma suna da haɗin-kai sosai kuma suna kula da juna,” in ji Halima.
Ta kuma kammala da cewa, “Kowane yaro na da halinsa na musamman. Wasu suna da kuzari da kuma bayyana kansu, yayin da wasu suke shiru kuma suna lura sosai. Abin ƙayatarwa ne ganin yadda suka bambanta, amma duk da haka suna danƙon zumunta.”















