"Mugun” burin Isra’ila na mamaye Gabas ta Tsakiya
Masana da ƙwararru da dama a faɗin duniya sun yi amannar cewa shigar Isra’ila cikin Lebanon da sunan yaƙi, ƙoƙari ne na cim ma “mummunan” burinta na mamaye ƙasar.
Mun yi nazari kan wannan buri na Isra’ila wato “Greater Isreal”, da inda take hanƙoron mamayewa a ƙasashen Gabas ta Tsakiya, tun daga Kogin Nilu har zuwa Kogin Euphrates, wato wuraren da suka hada da wasu yankunan Masar, Lebanon da Jordan, sai kuma daga kudancin Turkiyya har a dangana da ƙasar Saudiyya.