Barnar da hako fetur ke yi a Nijeriya
Hukumar Kula da Muhalli da Fetur ta Jihar Bayelsa (BSOEC), ta ce jihar na bukatar dala biliyan 12 don gyara da da farfado da kuma inganta muhalli da bangaren lafiyar al’umma da ayyukan hako man fetur da iskar gas suka yi wa illa a tsawon shekaru.
Rahoton da aka fitar, mai shafi 211, a ranar Talata mai taken: “Kisan kare dangin da ake wa muhalli: Lissafa asarar da hakar fetur ya jawo a Bayelsa, Nijeriya,” wani kundin bayanai ne kan shekara fiye da 60 da aka shafe ana ayyukan hakar mai a jihar da kamfanin Shell ya yi.