Tuni dai hukumomin Nijar suka sanar da shirinsu na ninka adadin sojojin ƙasar zuwa 50,000 daga yanzu zuwa shekarar 2025./Hoto:AFP

Rundunar sojojin Jamhuriyar Nijar ta ce za ta kafa runduna ta musamman da za ta kare "wurare na musamman", cikinsu har da wuraren haƙar ma'adinin yuraniyom da rijiyoyin man fetur, daga hare-haren 'yan ta'adda a ƙasar da ke fama da rashin tsaro tun 2015.

Rundunar ta musamman za ta "ƙarfafa tare da tabbatar da tsaro a wurare na musamman", a cewar Kanar Mounkaila Sofiani, shugaban fannin tsare-tsare na ma'aikatar tsaron Nijar, a wata sanarwa da ya karanto a gidan talbijin na ƙasar ranar Talata da maraice.

"Za a ɗauki matakin ne domin daƙile masu yi mana ƙafar-ungulu da masu kai hare-haren ta'addanci da ma haifar da sauran barazanar tsaro a wurare na musamman," in ji shi, inda ya ƙara da cewa wannan mataki martani ne ga "wata barazanar tsaro ta musamman".

Wuraren da za a ƙarfafa tsaro sun haɗa da wuraren haƙar yuraniyon da ke arewacin ƙasar da rijiyoyin man fetur da ke arewa maso gabashi da kuma musamman bututan man fetur masu tsawon kilimita kusan 2,000 da aka shimfiɗa daga Nijar zuwa gaɓar ruwa ta Seme da ke ƙasar Benin.

Kazalika rundunar za ta bayar da tsaro ga hanyoyi na musamman na shige da fice daga ƙasar irin su hanyar da ta tashi daga Lome zuwa Niamey daga birnin Ougadougou, a cewar Sofiani.

Ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa za a soma ɗaukar sojoji kimanin 10,000 da za su shiga rundunar ta musamman. Ana sa ran ɗaukar sojoji 100, 000 a rundunar daga yanzu zuwa shekarar 2030, in ji Kanar Sofiani.

Tuni dai hukumomin Nijar suka sanar da shirinsu na ninka adadin sojojin ƙasar zuwa 50,000 daga yanzu zuwa shekarar 2025.

Haka kuma an ƙara wa'adin ritaya ta wasu sojoji daga shekara 47 zuwa shekara 52 sannan an sake ɗaukar sojojin da ba su daɗe da yin ritaya ba domin su ci gaba da aiki.

Nijar na fama da hare-hare na ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da ke da alaƙa da Al-Qaeda da Islamic State a yankunanta da ke kan iyaka da Mali da Burkina Faso.

Kazalika tana ci gaba da fafutukar kawar da mayaƙan Boko Haram da ISWAP a yankin Diffa da ke kan iyaka da Nijeriya.

AFP