A ranar Talata ake gudanar da ƙaramar sallah a Jamhuriyar Nijar bayan hukumomi sun bayyana ganin jaririn watan Shawwal.
Ranar Litinin da maraice Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci ta Jamhuriyar Nijar ta ce an ga watan Shawwal a jihohi biyar na ƙasar.
Don haka ta bayar da umarni a gudanar da sallar idin ƙaramar sallah a ranar Talata, 1 ga watan Shawwal, 1445 daidai da 9 ga watan Afrilun 2024.
Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci ta yi roƙon Allah ya karɓi ibadun da aka yi a watan Ramadan, sannan ta yi kira ga ƴan Nijar su ci gaba da yi wa ƙasar addu'o'in fatan alheri.
Sai dai ba a ga watan Shawwal ba a galibin ƙasashen duniya abin da ya sa hukumomi suka ayyana ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu a matsayin ranar ƙaramar Sallah.
Ƙasashen da za su yi ƙaramar sallah ranar Laraba sun haɗa da Saudiyya da Falasɗinu da Nijeriya da Qatar, da Iraƙi da Kuwait, da Masar, da Syria, da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Wannan ne karo na farko da ƴan ƙasar Nijar za su yi bukukuwan ƙaramar sallah ƙarƙashin mulkin sojin na Janar Abdourahamane Tiani bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa gwamnatin farar-hula ta Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023.