An tsare Bazoum tare da matarsa Hadiza a fadar shugaban ƙasar da ke Yamai./Hoto: Fadar shugaban Nijar

Mambobi tara na ƙungiyar 'yan tawaye da ke neman a saki hamɓararren shugaban ƙasar Jamhuriyar Nijar sun miƙa wuya ga gwamnatin mulkin sojin ƙasar ranar Litinin, kamar yadda jami'an gwamnati suka bayyana.

An kafa ƙungiyar ta Patriotic Liberation Front (FPL) a watan Agustan 2023, wata ɗaya bayan sojoji sun kifar da gwamnatin farar-hula ta Mohamed Bazoum.

Tun daga wancan lokacin ake ci gaba da tsare Bazoum tare da matarsa Hadiza a fadar shugaban ƙasar da ke Yamai.

Sai dai wani jami'in gwamnatin jihar Agadez ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: "Tara daga cikin mayaƙan FPL sun tuba kuma sun miƙa makamansu a wurin wani biki da aka yi ranar Litinin a gaban Janar Ibra Boulama", gwamnan jihar Agadez.

Mayaƙan FPL sun soma ajiye makamansu ne a farkon watan da muke ciki sakamakon tattaunawa da suka yi da "wasu masi faɗa a ji a yankin", a cewar kafar watsa labarai ta Air-Info.

Ranar 1 ga watan Nuwamba, mai magana da yawun FPL Idrissa Madaki da mambobi uku na ƙungiyar sun ajiye makamansu daban-daban a garuruwa biyu kusa da kan iyakar Libya, a cewar rundunar sojin Nijar da kuma gidan talbijin na ƙasar.

A watan jiya, gwamnatin Nijar ta cire matsayin zama ɗan ƙasa ga shugaban FPL Mahmoud Sallah da wasu mambobi bakwai na gwamnatin Bazoum waɗanda ake zargi da "aikata ta'addanci".

Sallah ya ɗauki alhakin hare-haren da aka kai wa sojojin Nijar a yankin arewacin ƙasar tare da lalata babban bututun man da aka shimfiɗa zuwa Benin a watan Yuni.

Kazalika ya yi barazanar kai hari a wasu muhimman wurare.

Ita ma wata ƙungiyar 'yan tawaye ta daban mai suna Patriotic Front for Justice (FPJ) ta buƙaci a saki Bazoum.

A makonnin baya-bayan nan hukumomi a Nijar sun ƙara ƙaimi a yaƙin da suke yi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya, inda suka ƙara shingayen binciken ababen hawa da sanya ido sosai kan masu zirga-zirga a kan tituna.

AFP