Ƙungiyar ta ce ba ta ɗauki wannan mataki ba sai bayan da duk wani ƙoƙari na tattaunawa da gwamnatin da jami’anta na neman shawo kan matsalar ya ci tura.

Ƙungiyar masu aika rahotanni daga wajen Kano da ke ƙarƙashin ƙungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya ta ce ta yanke hukuncin ƙaurace wa al’amuran da suka shafi gwamnatin Jihar Kano ba tare da ɓata lokaci ba.

Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun shugabanta na Kano, Aminu Ahmed Garko, inda ta ce ta ɗauki matakin ne saboda rashin kyauta musu da ake yi.

“An ɗauki wannan matakin ne don mayar da martani kan irin rashin kyauta wa mambobin ƙungiyarmu da gwamnatin ke yawan yi a lokacin da suke gudanar da ayyukansu,” in ji sanarwar.

Sai dai zuwa lokacin wallafa wannan labari gwamnatin Jihar Kanon ba ta mayar da martani ba tukun.

Ƙungiyar ta ce ba ta ɗauki wannan mataki ba sai bayan da duk wani ƙoƙari na tattaunawa da gwamnatin da jami’anta na neman shawo kan matsalar ya ci tura.

Sanarwar ta ƙara da cewa “Mambobin ƙungiyar na ci gaba da fuskantar tsangwama da tsoratarwa, har ma da cin zarafi a yayin gudanar da ayyukansu.

“Akwai matuƙar damuwa musamman ganin yadda gwamnati ta fi fifita wadanda ba ƙwararru ba a kan ‘yan jaridar da suka samu horo, inda hakan ya sanya ya zama wata manufa ta jiha ta ware wadanda suka fi dacewa da yin aikin.

“A sakamakon haka, muna sanar da cewa ba za mu sake zuwa duk wani taro na ‘yan jarida ko halartar wani taro na gwamnati ko yin hira da jami’an gwamnati ba har sai mun ga wani sahihin gyara ga ‘yancin fadin albarkacin baki da tsaron lafiyar ‘yan jarida,” in ji Aminu Ahmed Garko.

Ƙungiyar ta umarci dukkan mambobinta da su bi wannan umarni wajen nuna fushinsu kan rashin kyautata musu da gwamnatin jihar Kano ke yi.

We believe that a free and independent press is essential to a functioning democracy, and we will not stand idly by while our members are mistreated and intimidated.

Mun yi imanin cewa 'yan jarida masu zaman kansu suna da muhimmanci ga dimokuradiyya, kuma ba za mu saka ido kurum ba yayin da ake cin zarafi da tsoratar da mambobinmu.

TRT Afrika