Rarara bai yi ƙarin bayani ba kan ko sai da aka biya kuɗin fansa kafin sakin mahaifiyar tasa./Hoto:Dauda Kahutu Rarara

'Yan bindiga sun saki mahaifiyar fitaccen mawaƙin nan na Hausa Dauda Kahutu Rarara, makonni bayan sun yi garkuwa da ita.

Rarara ne ya sanar da haka a saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Laraba da safe.

"Cikin yarda da amincin Ubangiji, mun samu dawowar Mama cikin aminci," in ji mawaƙin.

Ya miƙa "matukar godiya ga Ubangiji" sannan ya gode wa 'yan uwa da abokan "sana’ata" da masoyansa a faɗi duniya bisa addu'o'in da suka yi masa.

Rahotanni sun ce 'yan bindigar da suka sace ta sun nemi a ba su naira miliyan 900 a matsayin kuɗin fansa.

Sai dai Rarara bai yi ƙarin bayani ba kan ko sai da aka biya kuɗin fansa kafin sakin mahaifiyar tasa.

An sace Hajiya Halima Adamu ne a ƙauyen Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja a ƙarshen watan jiya.

Lamarin ya ja hankalin 'yan ƙasar sosai musamman masu amfani da shafukan sada zumunta.

Fitattun mutane ciki har da tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar na cikin waɗanda suka yi kira a saki mahaifiyar Rarara.

TRT Afrika