"A yayin harin, harbin ya samu wata taransufoma mai ƙarfin 330/132/33kV da ke girke a wajen har sai da ta yi bindiga,” in ji sanarwar. Hoto: TCN

Hukumar da ke Dakon Wutar Lantarki ta Nijeriya TCN ta sanar da cewa wasu ‘yan bindiga sun kutsa wata ƙaramar tashar dakon wutar lantarki da ake ginawa mai ƙarfin 330/132/33kV a Obajana da ke jihar Kogi.

Wata sanarwa da manajan watsa labarai na hukumar, Ndidi Mbah ya fitar a ranar Laraba, ta ce lamarin ya faru ne a ranar Talata 12 ga watan Nuwamba da misalin ƙarfe 11:55 na dare.

“Rahotanni daga masu tsaron wajen sun ce ‘yan bindigar sun buɗe wuta ne kan mai uwa da wabi, inda masu gadin suka tsere.

"A yayin harin, harbin ya samu wata taransufoma mai ƙarfin 330/132/33kV da ke girke a wajen har sai da ta yi bindiga,” in ji sanarwar.

A matsayin martani kan lamarin, TCN ta ce tana nazari kan irin ɓarnar da harin ya jawo ta hanyar haɗa kai da ɗan kwangilar da ke kula da aikin.

Wannan lamarin wani bangare ne na barnar da aka yi wa kayayyakin sadarwa a fadin kasar. An gina sabuwar tashar watsa wutar lantarki ta Obajana ne domin ta zama na’urar samar da wutar lantarki mai karfin 1X150MVA 330/132/33kV da za ta inganta samar da wutar lantarki ga jihar Kogi da kewaye bayan an kammala ta.

TRT Afrika