Arewa maso gabas na daga cikin yankunan da 'yan ta'adda suka addaba a Nijeriya. Hoto/Babagana Umara Zulum

Gwamnonin Arewa Maso Gabashin Nijeriya sun nuna damuwa kan yadda ‘yan bindiga ke hijira daga wasu sassa na Nijeriya zuwa yankin.

Gwamnonin sun bayyana haka ne a yayin taron gwamnonin shiyyar arewa maso gabas wanda aka yi a birnin Maiduguri.

Gwamnonin wadanda suka hada da na Adamawa da Bauchi da Barno da Yobe inda na Taraba da Gombe mataimakansu suka wakilce su, sun nuna jin dadinsu kan yadda ake samun nasara kan ta’addanci amma sun ce akwai sauran rina a kaba.

“Yayin da ake ganin nasarar da aka samu a kan ‘yan tayar da kayar baya, wani sabon salo na ‘yan bindiga na kara tsananta rashin tsaro a yankin.

“Sakamakon hadin gwiwar da sojoji ke yi domin fatattakar ‘yan bindiga daga sauran sassan kasar, a halin ‘yanzu ‘yan bindigan na kwararowa arewa maso gabas,” in ji sanarwar da gwamnonin suka fitar bayan taron.

Gwamnonin sun tabbatar da cewa lamarin ya fi addabar jihohin Gombe da Taraba.

Haka kuma sun bukaci gwamnatin tarayya ta yi gaggawar daukar mataki domin magance wannan matsalar.

Za mu hukunta sarakunan gargajiya

Yayin da suke tattaunawa kan matsalar tsaron wadda ta addabi yankin, gwamnonin sun ce suna sane da cewa wasu sarakunan gargajiya da sauran shugabannin al’umma suna taimaka wa ‘yan bindiga.

Gwamnonin sun zargi wasu daga cikin sarakunan gargajiya ta bai wa ‘yan bindigan wurin zama da taimako.

“Kungiyar ta yanke shawarar hukucta duk wani basaraken gargajiya ko shugaban al'umma da aka samu yana da alaka da 'yan bindigar,” in ji gwamnonin.

Haka kuma gwamnonin sun koka kan yadda ake samun masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida suna bazuwa a yankin.

Sun alakanta hakar ma’adinan da ake yi ba bisa ka’ida ba da kuma rashin tsaron da ya addabi yankin. Yankin Arewa Mao Gabashin Nijeriya na daga cikin yankunan da ke fama da matsanancin rashin tsaro a Nijeriya.

Rikicin kungiyar Boko Haram ya yi matukar lalata lamura a yankin musamman a Jihar Borno inda dubban mutane suka rasu miliyoyi kuma suka rasa muhallansu.

Ana fargabar a yayin da yankin ke fama da matsalar Boko Haram da ISWAP, kwararar ‘yan bindiga a can kan iya kara dagula lamura.

A ‘yan kwanakin nan sojojin kasar suna ta samun nasara kan ‘yan bindiga da kuma ‘yan ta’addan Boko Haram.

TRT Afrika