Jakadan Turkiyya a Nijeriya ya ce Turkiyya a shirye take ta tallafawa Nijeriya a bangaren yaki da ta'addanci. / Hoto: X

Rundunar sojin kasa ta Nijeriya ta sanar da ƙudurin ƙarfafa dangantaka da Kamfanoni Masana'atun Tsaro na Turkiyya don kokarin shawo kan ta'addanci.

An bayyana haka ne a wata sanarwa da aka wallafa a shafin X na hedikwatar rundunar sojin kasa ta Nijeriya a ranar Alhamis, wadda mai magana da yawun hukumar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar.

Sanarwar ta fito ne bayan wata ziyara da jakadan Turkiyya a Nijeriya, Hidayet Bayraktar ya kai wa Babban Hafsan Sojin kasa na Nijeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja a hedikwatar sojin da ke Abuja.

Ambasada Bayraktar ya bayyana cewa kamar Nijeriya, ita ma Turkiyya tana da ƙalubalen tsaro, musamman na ta'addancin ƙasa-da-ƙasa, inda ya ƙara da cewa ƙasashen biyu suna da kwatantawa.

Jami'in diflomasiyyar ya yi nuni da cewa hada gwiwar kasashen biyu zai daƙile ayyukan 'yan ta'adda a kasashensu, ta hanyar dauko darasi daga ƙwarewar da suka samu a baya.

Kasar Turkiyya a shirye take ta hada kai da Nijeriya a bangarorin tsaron kasa da fasaha da tattalin arziki, don yaki da ta'addanci da masu tayar da kayar baya.

Da yake mayar da jawabi, babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya yaba da irin alakar da ke tsakanin hukumar sojin Nijeriya da masana'antun kera makamai na Turkiyya, da sauran cibiyoyin kasar.

Shugaban sojin ya yi nuni da karbar fasahar ƙera makamai, da jinyar jami'an a asibitocin Turkiyya. Ya kuma ambaci cewa kwanan nan hukumar sojin Nijeriya ta karbi kayayyakin yaƙi daga Turkiyya don inganta ayyukanta.

Daga nan sai shugaban sojin Nijeriya ya bayyana kyakkyawan fatansa kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, wajen karfafa dakarunsu da kuma musayar bayanan sirri, da ƙwarewa.

TRT Afrika