Nijeriya da Afirka ta Kudu sun yi kira kan a tsagaita wuta a yaƙin da ake yi a Sudan.
Ƙasashen sun yi wannan kiran ne a yayin da ministocin harkokin wajen Nijeriya Yusuf Maitama Tuggar da kuma Ministan Harkokin Wajen Afirka ta Kudu Ronald Lamola suka gudanar da wata tattaunawa ta musamman a gefen taron Majalisar Koli ta Ƙungiyar Tarayyar Afirka da aka gudanar a birnin Accra na Ghana.
A wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar bayan tattaunawar, ministocin sun ce sun tattauna kan batutuwan da suka shafi nahiyar Afirka waɗanda suka haɗa da zaman lafiya da tsaro.
Ministocin sun jaddada buƙatar da ake da ita ta kawo ƙarshen yaƙin da ake gwabzawa a ƙasar nan take take.
“Kasashen biyu sun nuna matuƙar damuwa dangane da yaƙin da ake yi a Sudan. Ministocin sun yi kira kan a tsagaita wuta nan take domin kawo ƙarshen yaƙin da kuma buɗe ƙofa ga bayar da agaji ga jama’a,” in ji sanarwar.
Al'ummar Sudan na ci gaba da fama da bala'in yunwa sakamakon yaƙin da aka kwashe watanni 15 ana yi tsakanin Sojojin Sudan da rundunar kai ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces (RSF).
Hukumar Lura da Masu Ƙaura ta Duniya (IOM) ta ce yaƙin wanda aka soma a watan Afrilun 2023 ya raba mutum miliyan 7.7 da muhallansu sannan fiye da mutum miliyan 2 sun fice daga ƙasar zuwa maƙota don yin gudun hijira, kuma kashi 55 daga cikinsu yara ne.
Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya ce Sudan ce ƙasar da yaranta suka yin gudun hijira, inda aka ƙiyasta ce yara sama da miliyan 5 ne suka zama 'yan hijira.