An saki ɗaliban makarantar firamare da sakandare ta Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna waɗanda ƴan bindiga suka sace a farkon watan da muke ciki, a cewar gwamnan jihar.
Gwamna Uba Sani ya bayyana haka ne a saƙon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a yau Lahadi da asuba.
Gwamnan bai yi ƙarin bayani kan ko sai da aka biya kuɗin fansa kafin a saki ɗaliban ba, amma ya gode wa shugaban Nijeriya Bola Tinubu bisa tabbatar da ganin an sako su ba tare da "cutar da su ba."
"Ina miƙa godiya ta musamman ga shugaban ƙasarmu Bola Ahmed Tinubu, GCFR bisa bayar da muhimmanci kan tsaron lafiyar ƴan Nijeriya da kuma musamman tabbatar da ganin an saki ɗaliban makarantar Kuriga ba tare da an illata su ba.
A lokacin da ake tsare da ɗaliban, na yi magana da shugaban ƙasa sau da dama. Ya ji zafin da muke ji, ya rarrashe mu kuma mun yi aiki tare ba dare ba rana domin tabbatar da ganin an dawo da ƴaƴanmu," in ji Gwamna Uba Sani.
'Ceto mata 76 da maza 61'
Sai dai a nasa ɓangare, Daraktan watsa labarai na sojin ƙasar Manjo Janar Edward Buba ya yi ƙarin bayani dangane da ɗaliban da aka ceto a ranar Lahadin.
Ya bayyana cewa an ceto jumullar mutum 137 ne waɗanda suka haɗa da mata 76 da maza 61.
Duk da cewa shi ma Manjo Janar Buba bai bayyana ko an biya kuɗin fansar da ƴan fashin suka nema ba, amma ya bayyana cewa sojojin Nijeriyar sun yi haɗin gwiwa da hukumomin gwamnatin Kaduna inda aka gudanar da samame a dajin Zamfara wanda hakan ya kai ga ceto ɗaliban da safiyar Lahadi.
'Dabaru da tsare-tsaren gwamnati'
Gwamnan na Kaduna Uba Sani ya ce an saki ɗaliban ne sakamakon "dabaru da tsare-tsaren" da gwamnatinsa da kuma jami'an tsaron Nijeriya suka yi.
"Dole ne na yi godiya ta musamman ga ɗan'uwanmu, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha'anin tsaro Malam Nuhu Ribadu bisa shugabancinsa na gari. Ni da Malam Ribadu mun kwashe tsawon kwanaki ba tare da barci ba muna tsare-tsare da shiri na ayyukan jami'an tsaronmu, abin da ya kai ga samun wannan nasara," a cewar gwamnan Kaduna.
Kazalika ya miƙa ''godiya ta musamman ga sojojin Nijeriya bisa ƙwazo da jajircewa da sadaukar da kai don nuna cewa za a iya maganin masu aikata laifuka kuma a dawo da tsaro a garuruwanmu.''
An saki ɗaliban na Kuriga ne kwanaki kaɗan bayan sojojin Nijeriya sun sanar da kuɓutar da wasu ɗaliban tsangaya da ƴan bindiga suka sace a jihar Sokoto.
A farkon watan nan ne ƴan bindigar suka sace ɗalibai kusan ɗari uku a makarantarsu da ke Kuriga lamarin da ya sanya matuƙar fargaba a zukatan mutane musamman a Nijeriya.