Yadda sabon matakin CBN kan asusun ajiyar waje zai shafi 'yan Nijeriya da tattalin arziki

Yadda sabon matakin CBN kan asusun ajiyar waje zai shafi 'yan Nijeriya da tattalin arziki

CBN ya ce yanzu masu ajiyar kudin kasashen waje a asusunsu za su iya hada-hadar har dala dubu goma a rana.
Sabon tsarin CBN ya ce a halin yanzu za a iya hada-hadar kudin da ba su wuce dala dubu goma rana ba. Hoto/Reuters

Daga Mustapha Musa Kaita

‘Yan Nijeriya da dama musamman ‘yan kasuwa da masu hada-hada da kudaden kasar waje sun yi maraba da matakin Babban Bankin kasar na janye takunkumin da ya saka a baya kan iyakance kudin da za su iya cira a asusunsu na kudaden waje a bankunan kasar.

Babban Bankin Nijeriya ya fitar da sanarwar cewa a halin yanzu masu asusun ajiyar waje za su iya hada-hadar kudin waje da ta kai dala dubu goma.

Daraktan da ke kula da harkokin bankuna na CBN Haruna B. Mustapha ya bayyana cewa an bullo da wadannan sabbin tsare-tsare ne don kara inganta kasuwar hada-hadar kudaden waje da kawo daidaito a kasuwar.

Ko a makon jiya sai da CBN ya yi kokarin daidaita kasuwar bayan-fage da kuma farashin gwamnati ta hanyar karya darajar naira.

Me wannan sabon matakin yake nufi?

Ana ganin wannan matakin zai fi shafar ‘yan kasuwar Nijeriya da ke fitar da kaya zuwa kasar waje ko kuma da ke cinikayya da wasu kasashe kamar yadda masanin tattalin arziki Abdullahi Abubakar da ke Nijeriya ya shaida wa TRT Afrika.

Wannan matakin zai sa 'yan Nijeriya su yi hada-hadar kudi da ba su wuce dala dubu goma ba a rana

“Amfanin ɗaga wannan ka’ida shi ne a karfafa wa ‘yan kasuwa gwiwa masu fitar da kayan Nijeriya waje domin samun karin kwarin gwiwar yin hakan domin wancan tsarin na baya yana karya musu gwiwa.

“Ka fitar da kaya ka sayar an biya ka da dala to amma duk lokacin da ka ce kana bukatar dalarka sai a hana ka, wannan yana karya musu gwiwa," in ji shi.

'Sauki ga ‘yan Nijeriya'

Dakta Sanusi Dahiru Mohammed wanda masanin tattalin arziki ne a Kaduna da ke Nijeriya ya ce wannan matakin zai matukar kawo sauki ga ‘yan Nijeriya.

A cewarsa, a halin yanzu ba tare da bata lokacin ba ‘yan kasar za su iya ciniki ko saya da siyarwa cikin sauki da kudaden kasashen waje ba tare da wata wahala ba.

“Wannan mataki zai sa mutane su rinka ajiye kudaden kasar waje a cikin asusun ajiyarsu saboda an kara ainahin abin da za ka iya ajiyewa a kullum zuwa dala dubu goma.

“Ainahin ‘yan kasuwa na hakika masu saye da sayarwa da sarrafa kayayyaki a kamfanoni za su samu sauki da walwala wajen saye da sayarwa wanda ci-gaba ne ga kasuwanci da kuma irin riba da haraji da za a biya wanda ta nan ne gwamnati take samun kudin shiga,” in ji Sanusi Dahiru.

Ta ya wannan mataki zai shafi tattalin arzkin Nijeriya?

A cewar Abdullahi Abubakar, wannan matakin zai iya bunkasa tattalin arzikin Nijeriya sakamakon kayan kasar da za a rinka fita da su waje ana dawo da kudin cikin kasar wanda hakan zai kawo ci-gaba.

“Wannan matakin zai sa ‘yan kasuwa su rinka fitar da kayan Nijeriya waje suna tallata su kuma kayan Nijeriya na samun kasuwa,” in ji Abdullahi.

“Wannan samun kasuwar zai kara darajar kudin Nijeriya ya kuma kara wa kasar kudaden shiga da bunkasa asusun Nijeriya na kasashen waje da ake kira foreign account kuma zai bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.

“Idan za a ci gaba da fitar da kayan Nijeriya kamar yadda China take yi da sauran manyan kasashen duniya, hakan zai karfafa gwiwar kamfanoni da wadanda suke yin kaya da manoma domin su bunkasa aikinsu don akwai kasuwa a waje,” in ji shi.

An dai ta samun kwan-gaba-kwan-baya kan batun kasuwanci da kudaden kasar waje a Nijeriya sakamakon irin matakan da babban bankin kasar CBN ya dauka baya.

A kwanakin baya ne CBN din ya haramta sayar da kudaden waje ga ‘yan kasuwar bayan fage inda ya ce sai dai su koma bankuna su rinka saye.

Haka kuma CBN din ya saka takunkumi kan kudaden da za a iya hada-hada da su a asusun waje.

Sa’annan ya kara fito da wasu matakai da na daina amfani da katin atm na naira a kasashen waje.

TRT Afrika