Daga Mazhun Idris
A kasar da ta fi kowace yawan jama’a da karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika, hayaniya tamkar wani bashi ne da miliyoyin mutane ke biya, musamman wadanda suke zaune a cikin birane.
Tun daga kamfanoni zuwa cunkoson ababen hawa a birane kamar Legas wanda ya fi kowane birni yawan jama’a a kasar, na zama matukar abin hayaniya ga dodon kunnen jama’a.
“Muna fama da hayaniya mara misaltuwa a kullum,” kamar yadda wani mazaunin Legas Adebomeyin Oluwatosin ya bayyana.
Akasarin gidaje da wuraren kasuwanci a fadin Nijeriya na gudanar da ayyuka ne ba tare da wutar lantarki ba wadda ake samu ta kasa, wanda hakan ya sa ba su da wata hanya illa amfani da janaretoci masu kara.
Kwararru sun tabbatar da cewa hayaniya ko kara wadda ta wuce kima kan illata lafiyar bil adama, kuma akalla hayaniyar tana kawo cikas wurin aiki da kuma zamantakewa.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa duk wani sautin da ya wuce maki 65 a ma’aunin decibels (dB) ya zama hayaniya, “kuma zai zama mai illa idan ya wuce maki 75 a ma’aunin decibel (dB)".
Idan matakin ya kai 120db, zai zama “mai radadi ga kunne."
Dakta Murtala Uba Mohammed, wanda ya gudanar da bincike kan tasiri da fahimtar illar hayaniya a Kano – daya daga cikin birane mafi jama’a a Nijeriya – ya yi gargadin cewa mazauna birnin na fama da hayaniya ninkin baninki.
Illa ga makarantu
Dakta Murtala Mohammed wanda malami ne a bangaren ilimin kasa a Jami’ar Bayero da ke Kano, ya shaida wa TRT Afrika cewa akwai mazauna birnin da dama da ke zaune ne a yankunan da hayaniya ta wuce kima, idan aka kwatanta da tsarin Hukumar Lafiya ta Duniya.
Kamar yadda ya bayyana, hayaniya za ta iya zama tana da alaka da cututtuka da ke damun jama’a da suka hada da damuwa da ciwon zuciya.
Bincikensa ya bayyana cewa hayaniya ta fi fitowa ne daga bangaren sufuri da karar injinan kamfanoni da wuraren gine-gine.
Hidimomin kasuwanci da yawan jama’a na cikin sauran ababen, wadanda duka ya dora alhakinsu kan karancin tsarin birane da kuma rashin aiwatar da doka.
Dakta Murtala ya yi amfani da wata mita ta sauti wadda ya rinka daukar adadin hayaniya tsawon mako daga Disambar 2017 zuwa Fabrairun 2018 a wurare hudu na birnin.
Haka kuma ya dauki sauti daga wurare 15 a lokacin da ake cikin cunkoson ababen hawa uku, tsakanin karfe 8:00 na safe zuwa 10:00 na safe, da tsakanin 12:00 na rana zuwa 2:00 na rana da kuma tsakanin 4:00 na yamma zuwa 6:00 na yamma.
Odar motoci na daga cikin sautin da ya fi zama hayaniya a biranen Najeriya, kamar yadda Dakta Murtala ya bayyana a bincikensa.
Duk da cewa makarantu sun kasance wuraren da ba a cika samun hayaniya a Kano ba, amma bincike ya nuna cewa lamarin ya yi matukar tasiri a kansu, haka kuma irin hayaniyar da ake samu a kodayaushe za ta iya kawo cikas ga karatu.
Malamin ya bayar da shawara ga gwamnatin Nijeriya da ta “sa ido kan makarantu da samar da gundumomi na musamman domin makarantun gwamnatin da masu zaman kansu” don magance illar hayaniya kan wuraren karatu.
Ridwan Imam Salis, wani mazaunin birnin Kano, ya shaida wa TRT Afrika cewa ya samu sauyi kan “yadda nake ji da kunnena” kuma a wani lokaci ina samun ciwon kai daga irin hayaniyar da ake samu a unguwar Fagge, inda a nan yake aiki.
Doka ta haramta hayaniya a Nijeriya
Ridwan ya bayyana cewa bai kula da cewa yana fuskantar hayaniya a muhallinsa ba sai a 2020 a lokacin da kullen korona ya tilasta zirga-zirgar ababen hawa da sauran lamuran yau da kullum.
“Muhallin ya fi dadi da kwanciyar hankali. Sai dai hayaniyar ta dawo bayan dage dokar kulle ta korona,” in ji shi.
Hayaniya ko kuma sauti wanda ya wuce kima an haramta shi a Nijeriya inda har za a iya cin mutum tara ko kuma a rufe shi.
Hukumar da ke kula da ingancin muhalli ta Nijeriya NESREA ita ce ke da alhakin kula da sauti wanda ya wuce kima a kasar.
Manufofin hukumar sun bayyana hayaniya a matsayin duk wani sauti mara dadi da jama’a ba sa so wanda zai iya yiwuwa yana da illa mai tsawo ga lafiyar bil adama ko kuma muhalli.
Dokar ta bayyana cewa duk wani wanda ya saba doka “dole ne ya biya naira N5,000 a kullum idan yana aikata hakan bayan an same shi da laifi ko kuma ya biya tarar naira 50,000, ko kuma a rufe shi daurin da bai wuce shekara guda ba ko kuma a yi masa duka”.
Idan wani kamfani ne ya yi wannan laifin, “dole ne idan aka same shi da laifi ya biya tara ta naira N500,000 da kuma karin naira 10,000 a kullum idan ya ci gaba da aikata laifin”.
Sai dai dokar ta kasance kamar wasu dokoki da dama a Nijeriya, da wuya ake aiwatar da ita, haka kuma wadanda hayaniya ke damu abu ne mai wuya su kai kara ga hukumomi.
Saba doka da kuma karancin aiwatar da dokoki a Nijeriya ba wai sun tsaya bane kawai kan hayaniya, duk da cewa hukumomi bas u iya kokarinsu wurin ganin an bi doka.
Mazauniyar Legas Adebomeyin Oluwatosin ta ce “mutane da da dama ba su kai kara kan hayaniya sakamakon ba su san wurin da za su kai karar ba”.
Yadda hayaniya ke lalata kunne
Dakta Hassan Mohammed Garba wanda likita ne a birnin Bauchi da ke arewacin Nijeriya, ya bayyana cewa idan mutum yana cikin hayaniya a kullum, hakan zai iya lalata jinsa.
Hassan wanda shi ne daraktan asibitin Pahlycon ya kuma shaida wa TRT Afrika cewa da zarar dodon kunnen mutum ya lalace, wasu cututtuka kamar sankarau za su iya kama mutum.
Ya bayyana cewa mutane wadanda suke da ciwon kunne sun fi hatsarin shiga cikin irin wadannan matsaloli.
Wata likita Dakta Hidaya Danbatta na ganin cewa musamman mata da yara sun fi zama cikin barazanar illolin hayaniya.
Dakta Hidaya wadda likitar haihuwa ce a asibitin koyarwa na Abuja ta bayyana cewa, “Dole ne a hana yara zuwa wuraren da ake hayaniya da kuma zuwa wuraren masu hayaniya domin kare kunuwansu.
"Haka kuma akwai bukatar mata su san irin illolin da yawan sauti zai iya yi wa dan tayi.”
Karar sauti ta fi tafiya a cikin ruwa, a daidai lokacin da ‘yan tayi ke girma, akwai sauti mai cutarwa da zai iya ishe su sakamakon matsananciyar karar da ke fitowa daga muhallin da uwa take zaune.
Domin guje wa hakan, likitar ta bayar da shawarar amfani da abubuwan dode kunne da kuma abubuwan da za su iya hana hayaniya ratsa cikin gini domin rage lamarin.
Ta gargadi jama’a kan zuwa wuraren taro wadanda lasifikarsu ke da matsanaciyar kara.
Ta bayyana cewa akwai bukatar mutum ya rinka zuwa akai-akai duba lafiya domin gujewa samun matsalar kunne.
Mai bincike Mohammed ya yi kira da a yi dokoki masu tsauri a majalisa wadanda za a aiwatar da su ba da wasa ba kan batun amfani da muhalli domin rage hayaniya.
Kamar yadda ya bayyana, samar da kyakkyawan tsari zai hana gine-gine wadanda ba su da tsari na rage sautin da ke shiga cikin gida.
Ya kuma yi kira da a shuka Karin bishiyoyi a cikin birni sakamakon bishiyoyi na da tasiri kan bishiyoyi.