Bikin Girbin Sabuwar Doya biki ne da ake yi duk shekara na al'adar kabilar Ibo. Hoto: Gov Emeka Ihedioha/Facebook         

Tun daga watan Agusta zuwa farkon watan Oktoba, ana fara bukukuwa a yankin kudu maso gabashin Nijeriya. Bikin Girbin Sabuwar Doya biki ne da ake yi duk shekara na al'adar kabilar Ibo.

Sarakunan yankin suna sanya kayan al'ada da kuma wasu "dodanni" da ke yawo a kan tituna a wani salo na nuna al'ada a Bikin Girbin Sabuwar Doya, wani bangare na al'adar kabilar Ibo a yankin kudu maso gabashin Nijeriya.

Wannan wani bangare ne na Bikin Girbin Sabuwar Doya wanda hakan alama ce ta farawa da kuma kammala girbin doya.

Ta fuskoki da dama, biki ne na gode wa Ubangiji da nasarorin da aka samu da tallata al'adu da kuma ci gaban al'umma.

Ana fara bikin ne da yin addu'o'i daga nan ne sai a fara cin sabuwar doyar da aka girbe. Ana gasa doyar, sai a tsoma ta a cikin manja sannan a sanya ta cikin barasa.

A shekaru 10 da suka wuce, bukukuwan sun wanzu zuwa wasu yankuna, wasu da ke zaune a ketare suna da karsashin yin bukukuwan – daga Amurka har zuwa China.

Doya tana da alaka da al'adun Ibo. Hoto: Gov Emeka Ihedioha/Facebook

"Muna yin wadannan bukukuwan kowace shekara har tsawon shekara 11 yanzu," in ji Cif Godwin Anyaogu, Shugaban Kungiyar 'Yan Kabilar Ibo ta Ohaneze Ndi Igbo a kasar Ghana.

"A kowace shekara muna sanya bayanai: muna matukar alfahari da al'adunmu da yadda muke rayuwa. Bikin Girbin Doyan yana da muhimmanci a gare mu Ibo saboda yana nuna yadda muke ribatar aiki tukuru.

"Mun kwashe tsawon watanni muna aiki da girbi kuma yanzu muna farin ciki saboda mun samu amfani mai kyau," in ji shi.

Aiki mai daraja

Ana yi wa doya shagulgula – wacce ita ce babbar abinci a yankin – tana da muhimmanci a al'adance a yankin Ibo – shagulgula ne da ake yinsu a tsakanin al'ummomi daban-daban masu magana da harsuna fiye da 30, kamar yadda cibiyar harsuna ta duniya wato International Centre for Language Technology ta bayyana.

A tsarin al'adun kabilar Ibo, kalmar duniya (wadda ita ake kira Ala a harshen Ibo) abu ce mai muhimmanci sosai. Gwarzaye sun ce duniya ta ba al'ummar Ibo kyautar noman doya.

Ba shakka shi ya sa doya take taka muhimmiyar rawa a rayuwar Ibo. An yi amannar cewa abincin sarakuna ce, kuma tana taimaka wa wajen karya baki kuma tana da matsayi a addinance.

Al'ummar Ibo da ke zaune a wajen yankin suna Bikin Girbir Sabuwar Doya. Hoto: Gov Emeka Ihedioha/Facebook

Idan girbin doya ya yi kyau alama ce da ke nuna cewa shekara za ta yi kyau ga sauran amfanin gonar. Yayin Bikin Girbin Doya, ana martaba masu zuba jari da mutanen kirki da sauran mutanen da suka yi nasara a rayuwa.

Ana bai wa mutanen da suka cancanta sarautar gargajiya musamman 'yan kasuwa wadanda suka kafa masana'antu kuma suka samar da damarmaki ga al'ummarsu.

"A al'adance ya kamata ne a yi bikin girbin a kasar Ibo, sai dai akwai Ibo wadanda suke rayuwarsu a wasu wurare ba sa dawo gida.

"Saboda haka, bikin ya rikida zuwa biki da ake yinsa a ko ina a duniya," in ji Farfesa Chigozie Nnabuihe malami a fannin nazarin harshen Ibo da al'adu a Jami'ar Legas a Nijeriya.

"A al'adar Ibo, babban laifi ne kin yin bikin na shekara-shekara ko kuma alama ce ta rashin godiyar Allah wanda hakan zai sa shekara ba za ta yi kyau ba.

Tasirin Kasashen Yamma

Kamar sauran bukukuwan al'adu, Bikin Girbin Sabuwar Doya yana fuskantar tarin kalubale.

Yayin yanayin da ba a saba gani ba da yake mamaye duniya, ana rage mayar da hankali kan abubuwa tarihi.

Hakan ya fara yin tasiri kan yawan doyar da ake nomawa da kuma yawan mutanen da ke halartar bikin.

Ana nuna damuwa dangane da yadda al'adun kasashen yamma suka fara yin tasiri kan Bikin Girbin Sabuwar Doya. Hoto: Gov Emeka Ihedioha/Facebook

"Eh, muna fuskantar tasirin sauyin yanayi kan amfanin gonarmu. Hakan ba kawai yana shafar kasar gonarmu ba ne. Abu da ke shafar duka duniya," in ji Anayaogu.

"Damina ba ta zuwa da karfin da ta saba zuwa da shi, kuma manoma suna samun raguwa wajen amfanin gonarsu. Ko da yake muna da kwarin gwiwar cewa ba zai kai ga cewa yunwa ta kashe mutanenmu ba."

Wani kalubalen kuma shi ne na mamayar da al'adun Kasashen Yamma suke yi wa al'adun Afirka.

Yawancin matasa a birane sun taba jin bukukuwa kamar Bikin Girbin Sabuwar Doya, amma da zarar sun fara bibiyar wasannin nishadantarwar na duniya, sai su rage sha'awarsu ga bikin girbin doya.

Bunkasar tattalin arziki shi ma wani dalili ne da ke sa dubban mutane yin ci-rani a kowace shekara wanda hakan ke shafar al'adu kamar Bikin Girbin Sabuwar Doyar.

Tasirin kafofin sada zumunta

A shekarar 2022 kawai, Hukumar da ke Kula da Shigi da Fice ta Nijeriya ta ce fiye da mutum miliyan daya da dubu dari takwas ne suka karbi fasfo, wannan ne adadi mafi yawa da aka karba a shekara daya a tsawon shekara bakwai.

Bikin Girbin Doya yana kawo hadin kai tsakanin 'yan Nijeriya. Hoto: Gov Emeka Ihedioha/Facebook

Idan wannan ya ci gaba, bikin al'adu kamar Bikin Girbin Sabuwar Doya zai fada cikin hadari, in ji masana.

Wannan abin damuwa ne biyo bayan gargadin da Hukumar Ilimi da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta yi kan cewa harshen Ibo yana barazanar bacewa.

Akwai alamun gaskiya ga wannan zance ganin yadda matasan Ibo da yawa suna shan wahala wajen yin magana da harshen. Sai dai Anyaogu ya ce yana ganin Bikin Girbin Sabuwar Doya zai taimaka wajen raya al'adar yankin duk da cewa akwai tarin kalubale.

"Gurbatar al'adu babban abu ne, kuma wannan ne ya sa muka dukufa wajen bunkasa bikin a duk shekara. Ya kamata mu yi tsayuwar daka wajen ganin mun kawar da abin da ke dauke hankalin 'ya'yanmu, ta yadda za su rika ganin al'adunmu da suke da shafe su."

Bikin na baya-bayan ya samu matasa a inda suke: a shafin TikTok da Facebook da kuma Instagram kuma duk wata kafa babba ta sada zumunta.

Patrick Adigwe daga al'ummar Ibusa a jihar Delta a Nijeriya ba ya fasa yada a shafin YouTube. "Yada wa ya hanyar kafafen sada zumunta yana da muhimmanci saboda ya kamata mu bar wa 'yan baya wannan al'adar.

Wannan ba biki ne kawai ba a garemu, amma wani makami ne na hanyar tsiranmu," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika. Farfesa Nnabuihe yana da bayanan falsafa kan muhallin al'adu a wannan zamani.

"Jijiya tana tsurowa daga wurin da babbar bishiya ta fadi. Wannan ne tsarin rayuwa," in ji shi. "Muna da matasa da yawa wadanda suke kaunar al'ada, ba tare da la'akari da zamanin da suke ba.

"Su ne za su kasance masu tasiri wajen yada sakon Bikin Girbin Doya da sauran bukukuwan al'adun Afirka."

TRT Afrika