Malaman makarantar firamare da sakandaren da ƴan bindiga suka kai wa hari a jihar Kaduna da ke Nijeriya sun shaida wa gwamnatin jihar cewa ɗaliban da aka sace sun kusa 300.
Ƴan bindigar sun kai hari a makarantar da ke ƙauyen Kuriga a ƙaramar hukumar Chikun ranar Alhamis inda suka kwashi ɗaliban.
Wasu malamai da suka tsere tare da ɗaliban yayin da aka kai musu harin sun shaida wa gwamnan jihar Mallam Uba Sani, wanda ya ziyarci garin a ranar ta Alhamis, cewa ɗaliban da aka sace sun kusa 300.
Wani malami Sani Abdullahi ya ce an kwashi "ɗalibai 187 daga ɓangaren sakandare, sannan aka kwashe ɗalibai 125 daga ɓangaren firamare amma 25 sun dawo".
Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne bayan ya isa makarantar da kafin ƙarfe takwas na safe.
Malamin ya ce ya isa makarantar "da misalin ƙarfe 7:45 inda na shiga ofishin firinsifal wanda ya min na waiga baya. Ina juyawa sai na ga ƴan bindiga sun kewaye makarantar".
Ya ƙara da cewa sun faɗa cikin matuƙar rudani inda daga bisani suka tsere tare da wasu ɗaliban.
A jawabinsa, Gwamna Uba Sani, ya sha alwashin yin bakin ƙoƙarinsa don ganin an kuɓutar da dukkan ɗaliban.
"Mutanen ƙauyen sun shaida mini cewa ɗan bangar da ya tunkari yan bindigar ya rasa ransa. Na shaida wa shugaban ƙasa da Mai ba shi shawara kan sha'ann tsaro halin da ake ciki a Kuriga. Sun tabbatar mini cewa suna ɗaukar matakan da suka dace don ganin an kuɓutar da ɗaliban," in ji gwamnan a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X.