Manhajar WhatsApp na barazanar ficewa daga Nijeriya sakamakon umarnin da Hukumar kare masu sayen kayayyaki ta ƙasar (FCCPC) ta bai wa kamfanin Meta na ya biya tarar dala miliyan 220.
Lamarin ya biyo bayan wani bincike da hukumar FCCPC ta gudanar kan shafukan kamfanin Meta ciki har da Facebook da WhatsApp inda ta gano cewa sun karya dokar kasuwanci da ta kare sirrin masu amfani da manhajar a lokuta da dama.
Rahotoni daga majiyoyin kusa da kamfanin sun nuna cewa akwai yiwuwar Meta, kamfanin da ya mallaki WhatsApp ya janye ayyukansa daga Nijeriya.
Sai dai hukumar FCCPC ta ce Meta yana borin-kunya ne kawai domin zille wa biyan tarar da aka sanya masa.
''Kamfanin Meta ya karya dokokin kare sirri a Nijeriya, ciki har da na musayar bayanan ‘yan Najeriya ba tare da izininsu ba da kuma nuna wariya tsakanin 'yan ƙasar masu amfani da manhajar da take ɗdkar kasuwanc,'' a cewar wata sanarwa da Hukumar FCCPC ta wallafa a shafinta na X.
''Mataki na ƙarshe na buƙatar manhajojin da ke ƙarƙashin Meta su mutunta ƙa'idoji da dokokin Nijeriya ta tanada, ta hanyar daina amfani da damar da suka samu daga 'yan ƙasar da sannan su sauya ayyukansu don dacewa da ƙa'idodin Nijeriya tare da mutunta haƙƙin masu amfani da su,'' in ji sanarwar FCCPC.
Hukumar ta ƙara da cewa ''don hana saɓa ɗokoki a nan gaba da kuma tabbatar da an bi matakan amsa laifukan da ake zargin Meta, FCCPC ta sanya hukuncin biyan tara na dala miliyan 220''.
Kazalika hukumar ta ce ayyukanta sun dogara ne kan kare haƙƙoƙin masu sayen kayayyaki da bayanan sirrinsu, kana wannan mataki ne na tabbatar da an samar da ingantacciyar kasuwar zamani a ƙasar.
Nijeriya wadda ke da al'umma mafi yawa a nahiyar Afirka, tana da mutane sama da miliyan 103 da suka yi rajistar amfani da intanet a shekarar 2024, a cewar shafin DATAREPORTER a ƙasar, sannan mutane miliyan 36.75 ne suke amfani da kafofin sadarwa na intanet.
Kana mafi yawan al'ummar Nijeriya musamman masu ƙananan sana'o'i sun dogara ne da kafofin WhatsApp da Instagram da Facebook wajen tallata hajarsu ga kwastomominsu cikin sauki, ficewar kafar daga ƙasar za ta yi matuƙar tasiri kan masu amfani ita.