Victory Gbakara ya samu dala 129,000 saboda lashe gasar wannan shekara ta 'Nigerian Idols' da aka yi a ranar Lahadi. Hoto: Shafin Twitter/Victory Gbakara

Daga

Charles Mgbolu

Cikin yanayi na farin ciki Gbakara ya gode wa magoya bayansa bisa so da kauna da suka nuna masa bayan ya lashe gasar kai-tsaye ta rera waka ta 'Nigerian Idols' karo na takwas.

Shirin ‘Nigerian Idols’ kan zakulo hazikan mawaka masu baiwa ta rera waka, inda dubban mutane ke zuwa a tantance su kafin su samu damar shiga cikin gasar kadan-kadan.

Gbakara, mai shekaru 26, ya doke Precious Mac, mai shekaru 22, a matakin karshe na gasar da aka gudanar, inda ya karbi kyautar naira miliyan 100 da wata sabuwar mota. Kyautar ta kuma hada da yarjejeniyar nadar sauti da bidiyon waka.

Hawa da saukar murya

Magoya baya sun bayyana farin cikinsu game da nasarar Gbakara da Mac a shafukan sada zumunta, inda suka kira sautin muryarsu da mai ban mamaki da ratsa zuciya.

Wadanda suka shirya gasar sun sanar da sunan wanda ya yi nasarar lashe shirin na bana ta hanyar watsa labarin kai-tsaye da kuma ta intanet yayin da aka gudanar da bikin wasan wuta.

Matakin na karshe ya samu rera waka daga kungiyar ‘yan wasan da suka fafata a gasar ta bana, tare da alkalan shirin kamar su D’banj da Simi da Obi Asika, wadanda suka yi fice a fannin nishadantarwa a Nijeriya.

Shirin da aka kwashe makonni goma ana gudanarwa tun daga ranar 23 ga watan Afrilu zuwa 16 ga watan Yuli, fitaccen dan jarida a Nijeriya, IK Osakioduwa ne ya gabatar da shi.

Shirin Nigerian Idols wata gasa ce ta rera waka wacce ta shahara a fadin nahiyar inda miliyoyin masoya ke bibiyar ta a intanet.

Kamfanin watsa shirye-shirye na Africa Magic (MultiChoice) wanda ke daukar nauyin shirya gasar kyautar Africa Magic Viewers’ Choice Awards, mafi girma da shaharar shirin da ke ba da lamabar yabo na fina-finai da gidajen talabijin na tauraron dan adam a yankunan kudu da hamadar saharar Afirka.

Har ila yau, kamfanin shi ke daukar nauyin gudanar da shirin Idols a kasar Afirka ta Kudu wanda shi ma ake watsa shi a duk fadin nahiyar.

TRT Afrika