Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta sa hannu kan yarjejeniya tare da Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya, inda za ta bayar da dala miliyan 25 don samar da agajin abinci na gaggawa ga waɗanda rikicin Sudan da Sudan ta Kudu ya shafa, cewar rahoton Kamfanin Labarai na Daular.
Za a samar da tallafin kai-tsaye ga rukunin al'umma da rikicin ya shafa, ciki har da 'yan gudun hijira, da waɗanda yaƙi ya ɗaiɗaita, da waɗanda suka koma gida, cewar kamfanin labaran, a ranar Lahadi.
Tun tsakiyar watan Afrilun 2023 ne Rundunar Sojin Sudan da Rundunar Ɗaukin Gaggawa ta Sudan suka tsunduma yaƙi tsakaninsu, wanda ya haifar da mutuwar kusan mutum 15,000, da tagayyarar mutune da 'yan gudun hijira miliyan 8.5, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.
Sultan al Shamsi, mataimakin ministan harkokin cigaban ƙasashen duniya, shi ne ya sanya hannu kan yarjejniyar. Sai kuma Mathew Nims, babban daraktan ofishin Hukumar Abinci ta Duniya na Washington shi ma ya sanya hannu.
Yaɗuwa ƙasashe maƙwabta
A cewar kamfanin labaran, mutane miliyan 17.7 a Sudan da mutane miliyan 7.1 a Sudan ta Kudu suna fuskantar matsanancin rashin abinci sakamakon yaƙin a Sudan.
Don taimakawa wajen rage raɗaɗin rikicin, UAE ta sha alwashin bayar da jimillar kuɗi dala mailiyan $25 na agaji: wato dala miliyan 20 ga Sudan da kuma dala miliyan 5 ga Sudan ta Kudu.
Ranar Laraba, hukumar abincin ta ce, “Yayin da rikicin Sudan ke ci gaba, ana samun yaɗuwar matsala zuwa ƙasashe maƙwabta,” kuma ta ƙara da cewa, “daga kusan mutum miliyan biyu da yaƙin ya ɗaiɗaita kuma suke rayuwa a wajen iyakokin Sudan, sama da rabinsu na Chadi da Sudan ta Kudu, waɗanda ƙasashe ne da su ma suke fama da tasu yunwar.”
A shekarar 2011, Sudan ta Kudu ta ɓalle daga Sudan bayan wani zaɓen raba-gardawa da aka gudanar.