Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Nijeriya (EFCC) ta yi fatali da sabuwar ƙididdigar cin hanci da rashawa (CPI) da kungiyar Transparency International ta fitar, wadda ta sanya kasar a matsayi na 140 a cikin kasashe 180.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriyar ta ce ƙasar na samun cigaba sosai a yaƙin da take yi da cin hanci da rashawa.
"Babu wanda zai musanta" cewa Nijeriya ta " samu gagarumin cigaba a yaƙin da muke yi da cin hanci da rashawa," in ji kakakin EFCC, Olanipekun Olukayode, a wata sanarwa a ranar Laraba.
"Muna buƙatar cigaba da tafiya a kan wannan turba; muna buƙatar ƙarfafa kanmu; muna buƙatar sanya mutane su bi ka'ida da haɓaka ayyukanmu, kuma a ƙarshe za mu kai ga ci.
"Ko sun ba mu ƙima mai muhimmanci ko a'a, abin da ke da muhimmanci shi ne muna inganta ayyukanmu," Olukayode ya jaddada.
Kungiyar Transparency International ta ce a rahoton da ta fitar a farkon wannan watan, ta yi nazari kan yadda kasashen suka magance cin hanci da rashawa a tsawon lokaci, inda ya mayar da hankali musamman kan yadda cin hanci da rashawa ke yin tasiri a ayyukan sauyin yanayi. Ta bai wa Nijeriya maki 26 cikin 100.
Sai dai hukumar EFCC ta yi fatali da sakamakon rahoton, inda ta ba da misali da kama wasu ‘yan kasashen waje da ta yi, waɗanda suka fito daga kasashen da kungiyar Transparency International ta ce sun fi Nijeriya samun cigaba a yaƙi da cin hanci.
“A wani samame ɗaya, mun kama sama da mutum 790 da ake zargi, ciki har da baƙi 194 da suka hada da Turawa.
"Wasu daga cikin kasashen da ƙungiyar TI ta saka su a matsayin waɗanda suka fi Nijeriya a jerin nata, to mun kama ‘yan kasashen da laifin zamba a Nijeriya,” Olukayode ya bayyana.
Kakakin EFCC ya ƙara da cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa wajen yaƙi da masu son durƙusar da ƙimar ƙasar a irin wannan jeri na ƙasa da ƙasa, yana mai cewa abin da har yanzu ya fi muhimmanci a wajensu shi ne cigaba da inganta ayyukan cikin gida da kuma ƙara ƙima ga Nijeriya.