Gwamnatin Nijeriya karkashin jagorancin Bola Tinubu ta sanya sunan wasu filayen jiragen sama sunan fitattu da tsofaffin shugabanni a kasar.
Wannan yana kunshe ne a cikin wata takardar daga Ma'aikatar Sufurin Jiragen Sama a kasar wadda Daraktar Aikace-aikace Misis Joke Olatunji ta sanya wa hannu.
Sanarwar ta ce an yi hakan ne "a wani mataki na sauye-sauyen da ake wa fannin sufurin jiragen sama".
An sanya wa Filin Jirgin Saman Maiduguri sunan tsohon Shugaban kasar Muhammadu Buhari yayin Filin Jirgin Saman Port Harcourt aka sanya masa sunan tsohon dan kishin kasar Obafemi Awolowo.
Sai Filin Jirgin Saman jihar Nasarawa da aka sa wa sunan wanda ya kafa Daular Usmaniyya wato Shehu Usman Danfodiyo.
Kazalika Filin Jirgin Saman Benin an sanya masa sunan marigayi Sarkin Benin Oba Akenzua II, na jihar Ebonyi da aka sanya wa sunan tsohon Shugaban Majalisar Dattawan kasar marigayi Sanata Chuba Okadigbo.
Filin jirgin sama na Ibadan kuma aka sanya wa sunan tsohon Firimiyar Yankin Yammacin kasar Ladoke Akintola.
Ga cikakken jerin su:
1. Filin Jirgin Saman Akure – Olumuyiwa Bernard Aliu
2. Filin Jirgin Saman Benin – Oba Akenzua II
3. Filin Jirgin Saman Dutse – Muhammad Nuhu Sanusi
4. Filin Jirgin Saman Ebonyi – Chuba Wilberforce Okadigbo
5. Filin Jirgin Saman Gombe – Brigadier Zakari Maimalari
6. Filin Jirgin Saman Ibadan – Samuel Ladoke Akintola
7. Filin Jirgin Saman Ilorin – Gen. Tunde Idiagbon
8. Filin Jirgin Saman Kaduna – Hassan Usman Katsina
9. Filin Jirgin Saman Maiduguri – Gen. Muhammadu Buhari
10. Filin Jirgin Saman Makurdi – Joseph Sarwuan Tarka
11. Filin Jirgin Saman Minna – Mallam Abubakar Imam
12. Filin Jirgin Saman Nassarawa – Shehu Usman Dan Fodio
13. Filin Jirgin Saman Osubi – Alfred Diete Spiff
14. Filin Jirgin Saman Port Harcourt – Obafemi Jeremiah Awolowo
15. Filin Jirgin Saman Yola – Lamido Aliyu Mustapha