Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga jagororin addini da su daina tsine wa Nijeriya a yayin wa’azuzzukansu.
Da yake jawabi a waje taron buɗe-baki da sarakunan gargajiya da malaman addini a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja a ranar Alhamis da maraice, Tinubu ya jaddada muhimmancin jagororin addini wajen sauya aƙidun mutane da ɗabbaka son haɗin-kai a tsakanin ƴan ƙasa.
Shugaban ya nemi jagororin da su zamo masu yin suka mai ma’ana da za ta kawo gyara ga masu riƙe da muƙaman siyasa.
Kazalika Shugaban Ƙasar ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar mayar da ƙalubalen da Nijeriya ke fuskanta zuwa yanayi mai kyau.
Ya nanata cewa babu wani ɗan ta’adda da zai iya kayar da muradin ƴan Nijeriya baki ɗaya, duk yadda suke ƙoƙarin cin zarafin ƴan kasa da ba su ji ba ba su gani ba.
Taron buɗa-bakin ya samu halartar sarakunan gargajiya daga arewaci da kudancin ƙasar da kuma malaman addinin Musulunci da na Kirista.
Shugaban Tinubu ya kuma bukaci shugabannin gargajiya da na addinai da su ƙulla alaƙa mai ƙarfi da gwamnati domin daƙile ta’addanci da ƴan fashi da garkuwa da mutane da sauran laifuka a ƙasar nan.
“A jiya a Abuja na halarci jana’izar sojoji 17 da aka kashe a Okuama, jihar Delta. Na ga matansu masu ciki da yara ƙanana.
''Soyayyar al'umma tana hannunku. Ku yi wa ƙasarmu addu'a. Ku ilimintar da tarbiyyantar da yaranmu. Wa’azuzzukan da muke yi wa mutane a coci da masallatai suna da muhimmanci.
''Kada ku la'anci al'ummarku. Wannan ita ce ƙasarku; kar a yi Allah wadai da ita a cikin wa'azi, kada ku zagi ƙasar. Shugabanci na nufin kawo sauyi.
“A ce wannan shugaban ba shi da kirki, wannan ba laifi ba ne. Ku bari sai zaɓe na gaba sai ku sauya shi, amma ku daina la'antar ƙasarku. Kar ku zagi Nijeriya. Wannan kyakkyawar ƙasa ce.”
Sauran mahalarta taron a madadin dukkan ɓangarorin sun gode tare da yaba wa Shugaba Tinubu kan salon mulkinsa da suke ce “ya ɗauki hanyar sauƙaƙa wa ƴan Nijeriya.”
Da yake magana a madadin Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya bayyana kyakkyawan fatan da yake da shi cewa Nijeriya za ta koma kan turbar zaman lafiya mai ɗorewa.
Shi ma Apostle Samson Fatokun, Janar Sakatare na Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya ya ce sun gamsu da yadda gwamnatin Tinubu ke jajircewa wajen kawo ƙarshen satar mutane da fashi da makami da kuma ɗaukar mataki a kan masu aikata laifin.