Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya roƙi ƴan majalisar wakilan ƙasar su daina yawan kiran ministoci da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya don titsiye su a gaban kwamitocin majalisar.
A yayin da yake buɗe-baki da ƴan majalisar a ranar Laraba da maraice a fadar gwamnatin ƙasar, Shugaba Tinubu ya ce duk da cewa sa ido yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana a cikin harkokin mulki, yawan kiran jami’ai na iya kawo cikas ga ayyuka da kuma yi wa ƴan ƙasa hidima.
“Na daɗe ina kallon yadda kwamitoci daban-daban suke kiran ministoci da shugabannin hukumomi. Na yi wa Shugaban Majalisa ƙorafin cewa su bar su su sha iska. Su bar mutanen nan su yi aikinsu. Ba muna cewa ba ku da tasiri ba ne. Ba muna cewa ba za ku iya sa ido ba.
"Amma ku yi la'akari da aikin farko na kowace hukuma da ma'aikatanta, ko irin nauyin da ke kan Gwamnan Babban Banki ko Babban Ministan Tattalin Arziki da Ma'aikatar Kuɗi a gare ku da sauran al'umma baki ɗaya,” kamar yadda sanarwar da mai taimaka masa kan harkon watsa labarai ta ambato shi yana cewa.
Shugaban ƙasar ya buƙaci ƴan majalisar da su nuna hazaƙa wajen gudanar da ayyukansu na sa ido.
"Idan ana raba musu hankali ko damun su, wataƙila za mu sauya salon zaman majalisa zuwa cikin tsawon dare. Dole ne mu nemo hanyar da za mu yi mu’amala mai kyau da juna. Wannan roƙo ne gare ku.
"Ku duba ku ga ko za ku iya yarda su aika wakilai a wasu lokutan ko kuma su aike muku takardu,” in ji Shugaban ƙasar, yana mai roƙon majalisar wakilan a kan batun.
Yayin da yake bayyana ƙwarin giwar da yake da ita a kan Majalisar Dokoki ta ƙasa wajen tabbatar da shugabanci na gari, Shugaba Tinubu ya yaba da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin ɓangaren zartarwa da na majalisa.
Ya ce haɗin gwiwar aiki da aka samu ya haifar da gaggauta amincewa da wasu ƙudurori don inganta jin daɗin ƴan Nijeriya.
'Kar ku manta da mazaɓunku'
Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci ‘yan majalisar da kada su manta da mazaɓunsu, sannan su yi amfani da watan Ramadan wajen tausayawa da tallafa wa marasa galihu a cikin al’umma.
''Muna yin sadaukarwa ga ƙasar, kuma muna tabbatar wa ƴan ƙasar cewa za a ji daɗi a nan gaba. “Dole ne mu yi imani, kuma don Allah kar ku manta da mazaɓunku, ku tuna halin da suke ciki.
''Ba zan iya daina gode muku kan abin da kuke yi ba, amma ƙasarmu kuke yi wa hidima. Babu wanda yake yi wa kansa wannan abu. Na Nijeriya ne, kuma ba mu da wata ƙasa sai Nijeriya,” in ji Shugaba Tinubu.
Za a yi sojojin da aka yi wa kisan gilla jana'izar ban-girma
Kazalika, a wajen buɗe-baki, Shugaba Tinubu ya taɓo batun kisan gillar da aka yi wa wasu sojojin ƙsar 17 a Jihar Delta a makon jiya, inda ya sake miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan mamatam tare da yin alƙawarin cewa sadaukarwa da suka yi ba za ta tafi a banza ba.
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa za a yi wa jami’an jana’izar ban-girma da ta dace da kuma karramawar ƙasa.
''Sun gamu da ajalinsu a wajen yi wa ƙasa hidima. Mu yi aiki don tausayawa tare da nuna cewa sun cancanci sadaukarwar da suka yi wa Nijeriya.
Sojojin sun rasa rayukansu ne a yayin da suka kai ɗauki wurin da ake wani rikicin ƙabilanci a Ƙaramar Hukumar Bomadi ta Jihar Delta, inda "al'ummar yankin suka yi musu kisan gilla."
''Mun jinjina wa dukkan maza da mata masu aikin tsaro, muna kuma tausaya musu. Nan ba da jimawa ba zan yi ƙarin bayani, amma dole ne a yi musu jana'izar da ta dace da kuma karramawar ƙasa," in ji Shugaba Tinubu.
Shugaban Majalisar Wakilai
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Wakilan ya jaddada muhimmancin yin afuwa da karamci, da addu’a a cikin watan Ramadan, ya kuma yi kira da a hada kan al’umma da kuma goyon bayan Shugaba Tinubu.
“Ina so in yi kira gare mu da mu yi amfani da wannan wata wajen ƙara ayyukan alheri da kuma rage munanan ayyuka,” in ji shi.
Da yake tsokaci kan watanni 10 na wannan gwamnati, Shugaban Majalisar, Tajudeen Abbas ya bayyana cewa bangaren zartarwa da na majalisar dokoki sun ci gaba da aiki tare domin ci gaban kasa.
"Ya zuwa yanzu dai, majalisar na goyon bayan Shugaban Ƙasa da manufofinsa, kuma za mu ci gaba da tabbatar da cewa mun yi aiki tare," in ji Tajudeen Abbas.