Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon Gwamnan Babban Bankin Kasar, CBN.
Ya bayyana haka ne a sanarwar da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya fitar ranar Juma'a.
Olayemi Michael Cardoso ya maye gurbin Godwin Emefiele wanda Shugaba Tinubu ya dakatar daga mukaminsa kuma ake tuhumarsa da badakalar biliyoyin kudade.
Kazalika Shugaba Tinubu ya nada sabbin mataimakan gwamnan CBN guda hudu. Mutanen su ne Mrs. Emem Nnana Usoro, Mr. Muhammad Sani Abdullahi Dattijo, Mr. Philip Ikeazor da Dr. Bala M. Bello.
Labari mai alaka: Emefiele ya kashe tsarin hada-hadar kudin Nijeriya — Shugaba Tinubu
Gwamnan na CBN da mataimakansa za su yi wa'adi ne na shekara biyar, a cewar sanarwar.
Ta kara da cewa Majalisar Dattawan Kasar za ta tantance mutanen domin tabbatar da nadinsu.
A watan Yuni ne Shugaba Tinubu ya dakatar da Mr Emefiele daga shugabancin CBN, sannan ya bayar da umarni a gudanar da bincike a kan ofishinsa da kuma yadda ya tafiyar da sauye-sauye a fannin tattalin arziki.
Daga nan aka mika ragamar tafiyar da bankin a hannun mataimakinsa Mr. Folashodun Adebisi Shonubi don yin riko.
Tarihin Olayemi Cardoso
An haifi Cardoso a jihar Legas da ke kudancin Nijeriya kuma ya yi karatun firamare da sakandare a birnin na Legas.
Ya tafi Jami'ar Aston da ke Birtaniya inda ya yi digiri a fannin shugabanci a shekarar 1980. Ya kammala digirinsa na biyu a kan harkokin mulki daga Jami'ar Harvard Kennedy.
Sabon Gwamnan na CBN ya soma aiki a bankin Ctibank, kuma ya shugabanci bankin.
Ya kafa bankin Citizens International Bank, kuma ya shugabance shi tsawon shekara takwas.
Kazalika ya zama mamba na majalisar Koli ta kamfanoni masu zaman kansu da dama da suka hada da kamfanonin fetur na Chevron da Texaco.
Sannan ya yi aiki da Bankin Duniya da Majalisar Dinkin Duniya da Ford Foundation, da Hukumar Lafiya ta Duniya.
Cardoso ya zama Kwamashinan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Legas daga 1999 zuwa 2005 a zamanin da Bola Tinubu yake gwamna.
Ya yi aiki a matsayin mamba na majalisar bayar da shawara kan harkokin Kasafin Kudi da Tattalin Arziki a ofishin mataimakin shugaban Nijeriya daga 2015 zuwa 2019.