Shugaban sojin ƙasan Nijeriya, Laftar Janar Taoreed Lagbaja, ya rasu yana da shekara 56 a duniya.
Wata sanarwar da mai taimaka wa shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan watsa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce Janar Lagbaja ya rasu ne a Legas ranar Talata da daddare bayan jinya.
Lagbaja dai ya fara aikin soja ne a lokacin da ya fara karatu a makarantar hora da sojoji na Nijeriya da ke Kaduna a shekara 1987 kuma ranar 19 ga watan Satumban shekarar 1992 ne ya zama hafsa mai mukamin Lutanan Na Biyu.
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu na taya sojin Nijeriya da iyalan mamacin jimamin rashinsa.
Kwanan nan ne dai aka naɗa Manjo Janar Olufemi Oluyede a matsayin mukaddashin shugaban sojin ƙasa na Nijeriya, kuma jiya ne shugaba Tinubu ya ƙara masa girma zuwa mukamin Laftanar Janar.